NNPC: Sau 600 aka fasa bututun mai a bana kadai a Neja Delta

NNPC: Sau 600 aka fasa bututun mai a bana kadai a Neja Delta

- An fasa bututan mai sau 600 don satar mai

- Ana sa rai masu kokarin balla Najeriya ke wannan aiki

- Wasu kuma na ganin barayi ne kawai masu neman kudi

NNPC: Sau 600 aka fasa bututun mai a bana kadai a Neja Delta
NNPC: Sau 600 aka fasa bututun mai a bana kadai a Neja Delta
Asali: UGC

Kamfanin mai na NNPC, mai fidda man Najeriya, wanda dashi ta dogara kacokan don samar wa jihohi da tarayya kudaden da ake ayyuka da biyan albashi, tace a bana kadai, an fasa bututun mai sau 600 a yankunan da ake haqar man mai kawo kudi cikin sauki.

Man dai, danyen mai ne daga karkashin kasa, wanda mazauna yankunan kance nasu ne su su kadai, inda kuma sauran yankuna ke son a raba dasu.

Fasa bubutun mai yana jawo gobara, asarar mai, bata yanayi, da kauyukan wajajen, da ma samar da rashin tsaro a yankin.

DUBA WANNAN: Za'a sauke MBS daga Yarima mai jiran gado a Saudiyya

NNPC na kashe makudan kudade wajen liqe da gyara wuraren da man ya malala, wanda an shekara kusan 50 ana haqa.

Yanzu dai ana biyan wasu daga cikinsu kudaden da ake sa rai zasu hana su satar man, wanda ke jawo hadari ga kowa a yankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng