“Matawalle Ya San Komai”: Malamin Musulunci Ya Yi Tone Tone kan Yakar Yan Bindiga

“Matawalle Ya San Komai”: Malamin Musulunci Ya Yi Tone Tone kan Yakar Yan Bindiga

  • Yayin da ake shirin yakar yan bindiga a Arewa maso Yamma, malamin Musulunci ya soki tsarin Gwamnatin Tarayya
  • Sheikh Murtala Bello Asada ya ce bai kamata a bayyanawa duniya cewa jami'an tsaro suna shirin zuwa jihar Sokoto ba
  • Malamin ya ce karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle babu abin da bai sani ba game da ayyukan yan bindiga da ke faruwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan shirin Bello Matawalle na yakar miyagun 'yan bindiga.

Shehin malamin ya caccaki gwamnati inda ya ce ba da gaske ta ke yi ba saboda yadda suka sanarwa duniya shirinsu.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

Malamin Musulunci ya caccaki Matawalle kan yakar yan bindiga
Malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya ce gwamnati ba ta shirya yakar yan bindiga ba. Hoto: Murtala Bello Asada, Dr. Bello Matawalle.
Asali: Facebook

'Yan bindiga: Malamin Musulunci ya soki Matawalle

Sheikh Asada ya bayyana haka ne a cikin wani karatunsa da aka wallafa a shafin Sheikh Musa Lukuwa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasan kwaikwayo ake yi wallahi ba yakar su Bello Turji ake son yi ba, babu wanda ba a san inda ya ke ba saboda suna waya kowa ya sani."
"Kowa ya sani abin ya faru cewa motar sojoji ta makale wasan kwaikwayo ne, a dauka kafewa ta yi amma makaman da Turji ya dauka fa kowa ya ga abin da ya faru."
"Babu bambancin abin da Matawalle ya yi da masu ba da bayanan sirri ga yan bindiga, saura kwanaki biyu ya taho ya fito ya fadawa duniya."
"Matawalle ya sayi motoci ga yan ta'adda, daga cikinsu akwai Halilu Sububu da Ado Aliero da Bello Turji duk ya sayi mota kirar 'Hilux' ya ba su."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa ‘yan Arewa suka mamaye tawagar tsaron Tinubu, Matawalle ya magantu

- Sheikh Murtala Bello Asada

Malamin ya ce yan bindigar sun tsere

Malamin ya ce yanzu haka yan jihar Kebbi da Niger na kuka cewa yan bindiga suna shiga jihohinsu saboda duk sun tsere.

Shehin yake cewa an samu tabbaci daga cikin sojojin akwai wadanda aka dauka a 2023 wanda ko kukan bindiga ba su taba ji ba inda ya ce bai kamata a tura su tunkarar Turji ba.

Sheikh Asada ya soki mulkin Tinubu

Kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Malam Murtala Bello Asada ya magantu kan shirin zanga-zanga da aka yi a baya.

Malamin ya ce mutane su na cikin mawuyacin hali musamman a Zamfara da Sokoto da Katsina fiye da matsalar zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.