Sheikh Murtala Sokoto ya ce irinsu Isa Pantami su ka fi dacewa da shugabanci
Wani babban malamin addinin musulunci, Murtala Bello Sokoto ya fito ya koka game da halin da ake ciki a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Murtala Bello Sokoto a wajen darasi a kan babin zakkah da ya ke yi a majalisinsa a garin Sokoto, ya yi Allah-wadai da wahala da rashin tsaro da aka jefa al’umma.
A wani bidiyo da ya fito daga jaridar Sahara Reporters, an ji yadda wannan malami har ya kai ga yin kira ga shugaban kasa Buhari ya yi murabus idan ya gaza.
Malam Murtala Sokoto ya ce dama can Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani ya fadawa ‘Yan Najeriya cewa Buhari mai gaskiya ne irin na ‘Yan boko.
KU KARANTA: Tsohon bidiyon Pantami ya na kokawa da PDP lokacin karin kudin mai
A cewar Shehin, ana bukatar mutum mai gaskiya, kuma wanda ya fahimci ilmin addinin musulunci, ya ce a haka ne za a samu shugaba mai tausayin jama’a.
“Mu abin da mu ke cewa, Allah ya sa Janar Muhammadu Buhari ya gyara, Allah ya buda masa zuciya ya gyara, idan ba zai gyara ba, Allah ya kawo mana wani.”
Ya ce: “Wai akwai wata jam’iyya ta Manzon Allah ne? Babu wata jam’iyya ta manzon Allah, kowace jam’iyya akwai mutanen kirki, kuma akwai na banza.”
Ya tambaya, ya ce: “Jam’iyyar APC akwai mutanen kwarai ko babu? Jam’iyyar PDP akwai mutanen kwarai ko babu?” Mutane su ka amsa da cewa akwai!
KU KARANTA: Manufofin tattalin Buhari su na cin karo da juna - Shehu Sani
“Idan zan bada misali, sai in bada misalai da-dama, misali; akwai Malam Isa Ali Pantami. Mutumin kirki ne ko ba mutumin kirki ba?”
Wannan Malami ya ce Ministan sadarwar ya fi Buhari duk wata dabi’a da hali na kirki, don haka ya ce ire-irensa ya ke addu’a su karbi gwamnatin Najeriya.
“A jam’iyyar PDP akwai Yusuf Sambo Rigachikun. Irinsu mu ke so su karbi mulkin Najeriya.”
Kwanakin baya kun ji cewa a wani bincike da aka gudanar, an gano cewa ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami ya na cikin ministocin da su ka fi aiki a gwamnatin APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng