Yaki da Talauci: Tinubu Ya Yiwa Jihohi 34 Yayyafin N438bn Ana Shirin Zanga Zanga

Yaki da Talauci: Tinubu Ya Yiwa Jihohi 34 Yayyafin N438bn Ana Shirin Zanga Zanga

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta saki kudi har N438 biliyan ga jihohi 34 da babban birnin tarayya domin rage matsin tattalin arziki
  • Ta ware kudin ne a karkashin shirin NG-CARES wanda ta ce ta tantance jihohin a watan Janairu kuma ta saki kudin kwanan nan
  • Jihohin Zamfara, Nasarawa da Filato su ne suka fi samun kaso mai tsoka, Kaduna da Anambra kuwa ba su je an tantance su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta saki sama da Naira biliyan 430 domin jihohi 34 da babban birnin tarayya ƙarƙashin shirin NG-CARES.

Jami'in yaɗa labarai da sadarwa na sashen FCSU, Suleiman Odapu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Kara karanta wannan

NPA: Hukumar kula da tasoshin ruwa ta tatso harajin da ya dara na kowane shekara

Tinubu ya yiwa gwamnoni yayyafi kudi ana shirin zanga-zanga
Tinubu ya rabawa jihohi tallafin Naira biliyan 438 domin yaki da talauci. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu ya rabawa jihohi kudin NG-CARES

Sanarwar ta ruwaito shugaban shirin NG-CARES, Abdulkarim Obaje yana cewa an raba kudin ne bisa tantancewar aka yiwa gwamnatocin jihohi da tarayya a Janairun 2024 inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga sakamakon tantancewar, jihohi uku ke kan gaba wurin samun kudin. Zamfara ta samu Naira biliyan 48.2, Nasarawa Naira biliyan 27.2 da Filato Naira biliyan 26.3.

Sai dai, Obaje ya ce jihohin Kaduna da Anambra ne ba sunsamu halartar tantancewar ba wanda ya sa ba su samu ko sisi ba.

Ya bayyana fatansa na cewa dukkanin jihohi 36 da babban birnin tarayya za su shiga tantancewa ta gaba da za a yi a watan Satumban 2024.

"Manufar tallafin shirin NG-CARES" - Obaje

Shugaban shirin na NG-CARES ya ƙara da cewa an ba da tallafin kudin ne domin shirye-shiryen inganta zamantakewa da yaki da talauci a jihohin da babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Mista Obaje ya bayyana ƙwarin guiwarsa kan cewa kudin da aka fitar za a yi amfani da su ta yadda ya dace domin kawo sassauci ga rayukan talakawa a Najeriya.

Jaridar Tribune ta ruwaito Obaje ya miƙa godiya ga ministan kasafi da tsarin tattalin arziki, Abubakar Bagudu, kan yadda yake kula da shirin.

A cewarsa, wannan tallafin zai taimaka wajen zaburar da gwamnonin jihohi da ministan babban birnin tarayya wajen ingan rayuwar jama'arsu ta hanyar shirin NG-CARES.

Manyan jami'an gwamnati sun sa labule

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da wasu manyan jami'an gwamnati sun saka labule.

Sun hanzarta fadawa ganawar ne sakamakon shirin zanga-zanga da 'yan Najeriya suke yi kan yunwa da matsin rayuwa da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.