Gwamnatin Buhari: Nan da shekaru 2 za su azurta 'yan Najeriya sama da miliyan 40

Gwamnatin Buhari: Nan da shekaru 2 za su azurta 'yan Najeriya sama da miliyan 40

  • Gwamnatin Buhari ta bayyana aniyar tallafawa talakawa sama miliyan 40 domin cire su daga kangin talauci
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnati ta bayyana shirinta na NG CARES da ake shirin farawa nan kusa
  • Gwamnati ta ce, ta shirya yin wannan aiki ne cikin shekaru biyu masu zuwa domin rage radadin Korona

Ibadan, jihar Oyo - Gwamnatin tarayya ta fara kokarinta na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 40 daga matsanancin talauci nan da shekaru biyu masu zuwa ta hanyar shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya na COVID-19, NG-CARES.

Wannan na fitowa ne daga bakin kodinetan shirin na NG-CARES na kasa Abdulkarim Obaje a wajen rufe taron bita na tsawon mako guda a birnin Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnatin Buhari ta shirya azurta 'yan Najeriya
Mutum miliyan 40 zan cire daga talauci nan shekara biyu, inji Shugaba Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An yi wani taron horaswa ga sama da mutane 440 daga jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya a birnin Ibadan ta jihar Oyo.

Kara karanta wannan

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

Wadanda suka samu damar halartar taron sun hada wadanda jami’ai ne na sa ido da tantancewa a shirin, jagororin rarraba abubuwan shirin a jihohi da sassan kula a fadin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAN ta ruwaito cewa shirin na NG-CARES yana neman rage tasirin radadin Korona akan rayuwar talakawa, manoma, gidaje masu rauni, al'ummomi da kuma masu kananan masana'antu.

Mista Obaje ya ce shirin na NG-CARES ya fito ne daga gwamnatin tarayya, tare da goyon bayan bankin duniya tare da halartar gwamnonin jihohi 36.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa shirin zai yi tasiri ga halin da ake ciki na talauci a kasar nan, tare da daukar nauyin ‘yan Najeriya miliyan 40 kai tsaye da kuma a fakaice.

News Digest ta ruwaito shi yana cewa:

“Wannan dan karamin tallafi zai yi tasiri kai tsaye kan ‘yan Najeriya kimanin miliyan takwas zuwa 10 sannan kuma a kaikaice zai shafi mutane miliyan 20 zuwa 30.

Kara karanta wannan

Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

"Muna da kwarin gwiwa cewa hakan zai yi tasiri ga halin talauci a Najeriya bayan shekaru biyu."

Hakazlika, ya yi bayanin yadda shirin zai kasance, inda yace taron da aka yi nuna yadda jihohi a Najeriya suke a shirye domin aiwatar da shirin.

Yan Najeriya miliyan biyu zasu fara karɓan Biliyan N20bn wata-wata daga Yuni, FG

A wani labarin, gwamnatin tarayya tace zata fara raba wa yan Najeriya Naira Biliyan N20bn daga watan Yuni a tsarin tallafi karkashin shirin National Cash Transfer, kamar yadda Punch ta rahoto.

Bayanai sun nuna cewa FG zata biya yan Najeriya miliyan biyu N5,000 a shirin 'Basic Cash Transfer' da kuma ƙarin N5,000 a tsarin tallafawa talakawa. Jimulla FG zata kashe biliyan N20bn kan mutanen da zasu amfana.

Wani bayani da ya fita a watan Maris, 2022 kan dabaru da kuma tsarin harkokin ma'aikatar jin ƙai da walwalar al'umma ya nuna cewa yan Najeriya dake amfana da shirin ƙara ƙaruwa suke.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel