Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Ministocinsa, Ya Fadi Wadanda Zai Kora Daga Mukamansu

Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Ministocinsa, Ya Fadi Wadanda Zai Kora Daga Mukamansu

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta korar ministocin da suka gaza yin katabus a gwamnatinsa
  • Tinubu ya godewa duka ministocinsa saboda kokarin da suke yi sai dai ya ce zai sallami duk wanda ya gaza yin wani abin kirki ga ƴan Najeriya
  • Shugaban ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu yayin taro da shugabannin Arewa Consultative Forum

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai kori duka ministocinsa da ba su tabuka komai ba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa zai ci gaba da kawo ababan more rayuwa ga al'ummar Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tinubu ya bayyana dalilin kai gwamnonin jihohi 36 kotu

Tinubu ya tabbatar da zai kori wasu daga cikin ministocinsa
Bola Tinubu ya sha alwashin korar wasu daga cikin ministocinsa da suka gaza. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tinubu ya godewa ministocinsa kan kokarinsu

Tinubu ya fadi haka ne yayin hira da shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a fadarsa da ke Abuja, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya godewa duka ministocinsa da masu mukamai sai dai ya ce duk wanda ya gaza, zai raba shi da kujerarsa, Daily Post ta tattaro.

"Ina godewa duka ministocina da irin kokarin da suke yi, sai dai kuma duk lokacin da na fahimci sun gaza wurin bautawa ƴan Najeriya zan kore su."

- Bola Tinubu

'Gwamnoni na samun kudi" - Shugaba Tinubu

Tinubu ya roki gwamnoni da su inganta rayuwar al'umma musamman wurin amfani da kudin kananan hukumomi da gaskiya yadda ya dace.

"Ina rokonku da ku kira gwamnoni, ina iya bakin kokarina wurin tabbatar da samar da kudi ga Najeriya."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kuɗin 2024 a majalisar tarayya

"Dole su ma su tausaya wurin duba zuwa ga mutane da ke karkashinsu a wannan lokacin."

- Bola Tinubu

Tinubu zai sake gabatar da kasafin kudi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da karin kasafin kudin 2024 ga Majalisar Dokokin kasar nan.

Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a zaman haɗin guiwa a zauren majalisar datttawa ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da ƴan kasar ke kokawa kan halin kunci da tsadar kayayyaki da ake fama da shi musamman na abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.