Jerin Sababbin Ministoci 45 Da Mukaman Da Shugaba Bola Tinubu Ya Rabawa Kowa

Jerin Sababbin Ministoci 45 Da Mukaman Da Shugaba Bola Tinubu Ya Rabawa Kowa

  • An kirkiro sababbin ma’aikatun tarayya da Bola Tinubu ya rabawa duka Ministocinsa mukamai
  • Za a rantsar da majalisar FEC babu Malam Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete
  • Bello Matawalle zai zama karamin Ministan tsaro, Nyesom Wike zai kula da birnin tarayya Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Yanzu nan labari ya fito daga fadar shugaban Najeriya cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rabawa ministoci mukaman da za su rike.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya sanar da haka ga 'yan jarida a yammacin Laraba, za a rantsar da ministocin a ranar Litinin.

A rabon mukaman da aka yi, Nyesom Wike zai zama Ministan babban birnin tarayya Abuja, Ibrahim Geidam zai jagoranci ma'aikatar 'yan sanda.

Ministoci
Jerin Sababbin Ministocin Tinubu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Tinubu Ya Yi Koyi da Buhari, Ya Rike, Ya Hana Kowa Ministan Fetur

Ministoci da za su rike mukamai

  1. Hannatu Musawa – Ministar fasaha, al’adu da tattalin arzikin fikira
  2. Muhammad Badaru – Ministan tsaro
  3. Bello Matawalle - Karamin Ministan tsaro
  4. Yusuf T. Sunumu – Karamin Ministan ilmi
  5. Ahmed Dangiwa – Ministan gidaje da raya birane
  6. Abdullahi Gwarzo - Karamin gidaje da raya birane
  7. Atiku Bagudu – Ministan kasafi da tsara tattalin arziki
  8. Jihar Kaduna – Ministan muhalli
  9. Mariya Mahmud – Karamar Ministan Abuja
  10. Bello Goronyo - Karamin Ministan ruwa
  11. Abubakar Kyari – Ministan harkokin gona da abinci
  12. Tahir Mamman – Ministan ilmi
  13. Sa’idu Alkali – Ministan cikin gida
  14. Yusuf Tuggar – Ministan harkokin waje
  15. Ali Pate – Ministan lafiya da cigaban al’umma
  16. Ibrahim Gaidam – Ministan harkokin ‘yan sanda
  17. Maigari Ahmadu – Karamin Ministan karafa
  18. Shuaibu Audu – Ministan karafa
  19. Muhammed Idris – Ministan yada labarai da wayar da kai
  20. Lateef Fagbemi – AGF kuma Ministan shari’a
  21. Simon Lalong – Ministan kwadago
  22. Imman Suleiman Ibrahim – Karamar Ministar harkokin ‘yan sanda
  23. Zephianiah Jisalpo – Ministan harkoki na musamman
  24. Joseph Utsev – Ministan harkar ruwa
  25. Aliyu Sabi Abdullah – Karamin Ministan gona da abinci
  26. Festus Keyamo – Ministan harkokin jirgin sama
  27. Betta Edu - Ministar jin kai da yaki da talauci
  28. Heineken Lokpobiri – Karamin Ministan man fetur
  29. John Enoh – Ministan wasanni
  30. Nyesom Wike – Ministan birnin Abuja
  31. Bosun Tijjani – Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani
  32. Ishak Salako – Karamin Ministan muhalli
  33. Wale Edun – Ministan kudi da tattalin arziki
  34. Bunmi Tunji-Ojo – Ministan tattalin arzikin teku
  35. Adebayo Adelabu – Ministan makamashi
  36. Tunji Alausa – Karamin Ministan lafiya da kula da jama’a
  37. Dele Alake – Ministan ma’adanai
  38. Lola Ade-John – Ministan yawon bude ido
  39. Adegboyega Oyetola – Ministan sufuri
  40. Doris Anite – Ministar kasuwanci da hannun jari
  41. Uche Nnaji – Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire
  42. Nkiruka Onyejeocha – Karamar Ministan kwadago da samar da ayyuka
  43. Uju Kennedy – Ministar harkokin mata
  44. David Umahi – Ministan ayyuka
  45. Ekperikpe Ekpo – Karamar Ministar gas
  46. Abubakar Momoh – Ministan matasa

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kamfanin NNPC Ya Karbo Bashin Dala Biliyan 3 Don Inganta Farashin Naira, An Fadi Yadda Za A Biya Kudin

An ga Atiku wajen Kwankwaso

Daga baya an ji yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Atiku Abubakar bayan an yi watsi da jam'iyyar NNPP wajen rabon mukamai.

Yayin da Abdullahi Ganduje ya hadu da Nyesom Wike, tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya hadu da madugun Kwankwasiyya a gida a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel