Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2024 a Majalisar Tarayya

Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2024 a Majalisar Tarayya

  • Bola Ahmed Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kudin 2024 ga majalisar wakilan tarayya nan ba da jimawa ba
  • Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a jawabinsa ga 'yan majalisar yayin zaman haɗin guiwa ranar Laraba, 29 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa a lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke cika shekara guda da kafuwa bayan karɓar mulki a Mayun 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Nan ba da jimawa ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da karin kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin kasar nan.

Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a zaman haɗin guiwa a zauren majalisar datttawa ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Shugaba Bola Tinubu.
Bola Tinubu na shirin miƙa daftarin ƙarin kasafin kudin 2024 ga majalisar tarayya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Shugaba Tinubu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na kawo maku kasafin kuɗi a baya kuma kun amince da shi. Yanzu haka muna kan aiki nan ba da jimawa ba zan kawo daftarin (ƙarin) kasafin kuɗin 2024."

Akpabio ya mayar da martani

A martanin da ya mayar, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce:

"Mun gode mai girma shugaban kasa, za mu yi dakon karin kasafin kudi na 2024 da wuri-wuri."

Har ila yau, a wurin zaman hadin gwiwa wanda ya yi daidai da cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya, shugaban kasar ya tabbatar da sauya taken Najeriya, Leadership ta ruwaito.

Tinubu ya jadadda bukatar haɗa kai

Shugaba Tinubu ya roki majalisar dattawa da ta wakilai su ci gaba da aiki tare, su hada kai da gwamnati wajen gina kasar nan a kan turbar ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

"Ba mu da wani zaɓi, kasarmu ce, babu wanda zai zo ya taimaka mana idan ba mu tashi mun taimaki kanmu ba. Duk wani agaji da zai zo daga ƙasashen waje, sai da suka fara daga kansu.
"Don haka ya kamata mu haɗa kanmu wuri ɗaya mu gina kasar nan kamar yadda muka fara, ba don kanmu kaɗai ba, har da jikokin mu masu zuwa."

Majalisa za ta bincike korar ma'aikata

A wani rahoton kuma majalisar wakilan tarayya za ta gudanar da bincike kan korar ma'aikata sama da 600 a babban bankin Najeriya (CBN).

Majalisar za ta binciki yadda aka yi aka rubutuwa ma'aikata akalla 600 takardar kora a CBN bayan ta amince da wani kudiri da aka gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel