CBN Ya Lissafo Jerin Hada Hadar Kudi 16 da Harajin 0.5% Ba Zai Shafa Ba

CBN Ya Lissafo Jerin Hada Hadar Kudi 16 da Harajin 0.5% Ba Zai Shafa Ba

  • Bayan kawo dokar cire wani kaso a asusun bankunan 'yan Najeriya, bankin CBN ya yi karin haske kan tatsar harajin
  • Bankin ya lissafo wasu hada-hadar kudi 16 da wannan doka ba za ta shafa ba domin biyan kudin tsaron yanar gizo
  • Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafe da ake yi a kan wannan sabuwar doka da babban bankin CBN ya kawo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban bakin Najeriya ya bayyana sabuwar doka kan cire kudin haraji a bankunan 'yan Najeriya.

Babban bankin ya umarci dukkan bankuna su rika daukar 0.5% bayan hada-hadar kudi domin inganta tsaron yanar gizo.

CBN ya jero hada-hadar kudi da tsarin harajin 0.5% ya tsallake
Bankin CBN ya yi karin haske kan hada-hadar kudi da tsarin harajin 0.5% zai shafa. Hoto: CBN.
Asali: Getty Images

Wace doka CBN ya kawo a Najeriya?

Kara karanta wannan

Kamfani ya maka ma'aikata 2 gaban kotu bisa zargin satar biredin N2,600

Sabuwar dokar za ta fara aiki ne nan da makwanni biyu kamar yadda darektan tsare-tsaren kudi a CBN, Haruna Mustapha ya tabbatar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma daga ciki akwai hada-hadar kudi 16 wadanda wannan mataki ba zai shafe su ba, cewar rahoton Vanguard.

Hada-hadar kudi da ba su a tsarin CBN

Wadannan hada-hada sun hada da:

1. Biya da karbar bashi

2. Biyan albashi

3. Tura kudi tsakanin bankuna ga asusu mallakin mutum daya

4. Tura kudi ga kwastoma da kuke amfani da banki daya

5. Tura kudi zuwa CBN ko turo kudi daga CBN

6. Tura kudi zuwa wani a cikin banki

7. Gyara kan takardar cire kudi na banki

8. Takardun karbar bashi

9. Ajiyar kudi a tsarin zuba hannun jari

10. Kudin Fansho

11. Tura kudi zuwa kungiyoyi masu zaman kansu (NGO) da sauran hukumomin ba da tallafi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta kuma juyowa kan 'yan Kirifto domin inganta Naira a Najeriya

12. Biyan kudin makarantar ɗalibai

13. Hada-hadar kudi a asusun bankuna da ke ajiya

14. Sauya asusu tsakanin bankuna

15. Sa sauran dokokin bankuna ga kwastomominsu

CBN ya umarci zaftare 0.5% a bankuna

Kun ji labari cewa babban bakin Najeriya, CBN ya sake kawo sabuwar doka domin cire kudi yayin tura kudi zuwa asusun banki.

Bankin ya umarci bankuna su rika cire 0.5% a duk hada-hadar kudi da za a yi tsakanin kwastomomi domin tsaron yanar gizo.

Tuni 'yan Najeriya suka fara korafi ganin irin dokokin da gwamnati ke kakabawa jama'a duk da halin da ake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel