Ondo: Jam'iyyar APC Ta Ayyana Zaben Fidda Gwanin Jihar 'Inconclusive', Ta Fadi Dalilai
Yayin da ake gudanar da zaben fidda gwani a jihar Ondo, jam'iyyar APC ta ayyana zaben wanda bai kammala ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Jam'iyyar APC ta ayyana zaben fidda gwanin jihar Ondo wanda bai kammala ba.
Jam'iyyar ta dauki matakin ne bayan samun rahotanni daga unguwanni 203 da kuma kananan hukumomi 18.
![APC ya ayyana zaben fidda gwanin jam'iyyar wanda bai kammala ba APC ya ayyana zaben fidda gwanin jam'iyyar wanda bai kammala ba](https://cdn.legit.ng/images/1120/3fef811bbc73e8fe.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Wane mataki APC ta dauka kan zaben?
Shugaban kwamitin zaben fidda gwanin, Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi shi ya tabbatar da haka, cewar rahoton AIT.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ododo ya ce zaben bai gudana ba a wasu ƙananan hukumomi saboda rashin kawo kayan zaben da kuma masu gudanarwa saboda wasu matsaloli.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/b4d558a6e716438d.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa
Ya ce za a gudanar da zaben fidda gwanin a unguwannni 13 da ke karamar hukumar Okitipupa da misalin karfe 12:00 na a yau Lahadi 21 ga watan Afrilu.
Yankin na dauke da mambobin da suka yi rijista da suka kai akalla 9,515 wadanda za su gudanar da zaben a karamar hukumar, cewar Premium Times.
A jiya ne wasu miyagu suka tarwatsa zaben fidda gwanin da ake yi a Ward 1 da ke karamar hukumar inda suka lalata komai.
Fasto ya yi hasashen zaben Ondo
Har ila yau, Shugaban cocin Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen abin da zai faru a zaben jihohin Edo da Ondo.
Faston ya yi hasashen ne bayan wakilin jaridar Punch ya yi masa tambaya a wata tattaunawa da suka yi.
Wannan hasashe na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanya watan Satumba domin zaben jihar Edo yayin da za a yi na jihar Ondo a Nuwamba.
Tsagin APC ya dakatar da Ganduje
A wani labarin, kun ji cewa, an samu sabuwar takaddama yayin da tsagin jam'iyyar APC a matakin unguwa ya sake dakatar da Abdullahi Ganduje a jami'yyar.
Jam'iyyar ta dauki matakin ne bayan wani tsagin jam'iyyar a Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ya musanta dakatar da Ganduje.
Sakataren jam'iyyar a gundumar Ganduje, Ja'afar Adamu Ganduje shi ya tabbatar da haka inda ya ce suna zargin Ganduje da wasu zarge-zarge.
Asali: Legit.ng