InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Shehun Borno Ya Rasa Babban Ɗansa a Maiduguri

InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Shehun Borno Ya Rasa Babban Ɗansa a Maiduguri

  • Shehun Borno, marigayi Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi ya tafka babban rashi bayan rasuwar ɗansa a jihar Borno
  • An sanar da mutuwar Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da jinya
  • An sanar da lokacin yin sallar jana'izarsa wanda za a yi a yau Lahadi 28 fa watan Afrilu sa misalin karfe 4:00

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar babban ɗan marigayi Shehun Borno, Shehu Mustapha Umar El-Kanemi.

Marigayin Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi ya rasu ne a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi ta'aziyya yayin da tsohon sanata da ɗan uwan tsohon hadiminsa suka rasu a Kano

Shehun Borno ya tafka babban rashi a rayuwarsa
Babban ɗan Shehun Borno ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Asali: Twitter

Yaushe ɗan Shehun Borno ya rasu?

Zagazola Makama ta tabbatar da cewa Marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri bayan ya sha fama da jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsa, Shehu shi ne ke rike da saraurar karamar hukumar Marfe da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya, cewar Platinum Post.

Za a yi salla jana'izarsa a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00 a kofar gidansa da ke unguwar Limanti.

Tsohon shugaban NLC ya rasu a Borno

Har ila yau, Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ali Chiroma, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Borno.

Chiroma ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke Maiduguri, babban birnin jihar a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Katsina: An shiga makoki bayan 'yan bindiga sun hallaka shugaban APC da wani mutum

Yan sanda sun bindige soja a Borno

A wani labarin, kun ji cewa Hankula sun tashi a fadar Shehun Borno da ke Maiduguri bayan wani dan sanda, Donatus Vonkong ya harbe sojan da ke aiki da Operation Hadin Kai.

Majiyoyi da yawa sun sanar da cewa a ranar Laraba dan sandan ya sha giya ne lokacin da ya aikata wannan abin takaici.

Matasa sun yi saurin fara farautar ‘yan sanda a wurin amma sojoji sun dakatar da su inda suka ce hakan ba zai kawo gaba tsakanin jami’an tsaron ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel