Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

  • Hankula sun tashi bayan wani dan sanda, Donatus Vonkong ya harbi wani sojan da ke aiki da Operation Hadin Kai a cikin fadar Shehun Borno da ke Maiduguri
  • Majiyoyi da dama wadanda suka tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba sun ce sai dan sandan ya sha giyarsa ya yi tatil sannan ya yi aika-aikar
  • Hakan ya janyo matasa suka fara kai wa ‘yan sanda farmaki amma take anan sojoji suka bukaci kowa ya dakata don hakan bai isa ya janyo gaba tsakanin jami’an tsaron ba

Borno - Hankula sun tashi a fadar Shehun Borno da ke Maiduguri bayan wani dan sanda, Donatus Vonkong ya harbe sojan da ke aiki da Operation Hadin Kai.

Majiyoyi da yawa sun sanar da Daily Trust a ranar Laraba cewa dan sandan ya sha giya ne lokacin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An bindige gawurtattun yan bindiga uku har Lahira

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno
Hankula sun tashi bayan Ɗan sanda ya bindige soja a fadar Shehun Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasa sun yi saurin fara farautar ‘yan sanda a wurin amma sojoji sun dakatar da su inda suka ce hakan ba zai kawo gaba tsakanin jami’an tsaron ba.

Dama ba wannan bane karon farko

A shekarar da ta gabata, rundunar sojin Najeriya ta yi korafi akan yadda ‘yan sanda suke azabtar da wasu jami’an ta.

A wata takarda ta ranar 23 ga watan Nuwamban 2021, shugaban rundunar sojin kasa ya bukaci sojojin da ke aiki a yankuna daban-daban da su gabatar da sunayen sojojin da ‘yan sanda suka cutar.

Yayin da aka nemi tattaunawa da darektan labarin sojin, Manjo Janar Jimmy Akpor ya sanar da Daily Trust cewa wannan lamarin ba ya nuna rashin jituwa tsakanin jami’an tsaron, wani abu ne na daban.

A cewar kakakin sojin, akwai hanyoyin da za a bi wurin bullo wa matsalolin jami’an tsaron inda ya ce za a yi bincike sosai don gudun lamarin ya maimaita kansa.

Kara karanta wannan

Katsina: An kama boka da ke yi wa 'yan bindiga asiri da addu'oin samun sa'a

Bayar da tsaro sojoji da ‘yan sanda suke yi tare, don haka ba rashin jituwa bane ya janyo wannan lamarin

A cewarsa:

“Idan irin haka ya auku, yawanci tsautsayi ne amma akwai hanyoyin da ake bullowa. Hakan ba ya nuna rashin shiri tsakanin jami’an tsaron. Wannan abu ne na daban kuma muna amfani da salo na daban.
“Na tabbatar Operation Hadin Kai zata tabbatar ta yi binciken da ya dace don gudun hakan ya maimaita kansa. Abinda ya fi komai muhimmanci shi ne kare faruwar lamarin.
“Akwai dabarun da ake bi idan irin hakan ya faru, hakan ba ya nuna rikici tsakanin sojoji da ‘yan sanda. Tunda dama duk suna aiki tare ne wurin yaki da ta’addanci.”

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel