Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

- Fursunoni a gidan yari na Kano sunyi yunkurin tserewa a yammacin ranar Alhamis

- Musbahu Nasarawa, kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano ya tabbatar da hakan

- Nasarawa ya ce hargitsin ya tashi ne yayin da jami'an gidan suka yi kokarin kwace wasu haramtattun kaya daga hannun fursunoni

Jami'an tsaro, a yammacin ranar Alhamis sun dakile wata yunkuri da fursunoni suka yi na tserewa daga gidan gyaran hali na Kurmawa da ke kusa da fadar Sarki a jihar Kano, The Cable ta ruwaito.

An ji harbe-harben bindiga a kusa da unguwa da inda gidan gyaran halin ya ke a yayin da mutane ke shirin yin bude baki a yammacin ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Sunayen sabbin alƙalai 18 da Buhari ya amince da naɗinsu a kotun daukaka ƙara

Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano
Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Musbahu Nasarawa, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran hali na Kano ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wasu fursunonin sun so tada hargtsi ba su yi nasara ba.

"Mun dakile yunkurin da taimakon jami'an gidan gyaran halin," in ji kakakin hukumar.

Nasarawa ya ce hargitsin ya tashi ne a lokacin da jami'an gidan gyaran halin suke kokarin kwato wasu haramtattun kayayyaki daga hannun wasu fursunoni.

DUBA WANNAN: Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

Da farko, rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce fursunonin sun tada hargitsi ne saboda rashin samun abinci mai kyau yayin bude baki. Don haka suka yi yunkurin fitowa su sha ruwa a waje a ranar Alhamis.

Amma, Nasarawa, ya musanta wannan ikirarin da aka yi cewa rashin abinci mai kyau ne ya janyo hargitsin.

Ya kara da cewa a halin yanzu komai ya lafa kuma babu wani fursuna da ya tsere.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel