Yan fursuna sun tarwatsa gidan Yari, sun fantsama cikin gari

Yan fursuna sun tarwatsa gidan Yari, sun fantsama cikin gari

Babban kwantrolan hukumar kula da gidajen yari na kasa, Jafaru Ahmed ya bayyana sama da mazauna gidan yari su 40 sun tsere daga gidan Yarin garin Ikot Ekpene na jiha Akwa Ibom.

Daily Trust ta ruwaito Ahmed yana fadin cewa wannan lamari ya faru ne a ranar 27 ga watan Disambar shekarar data shude, inda ya danganta hakan ga sakacin jami’an hukumar dake gadin Kurkukun.

KU KARANTA: Mabiya addinin Shi’a sun y kira ga Buhari da babban murya

“Sama da mutane 40 ne suka tsere daga Kurkukun Ikot Ekpene da misalin karfe 11.45 na safiyar ranar 27 ga watan Disamba a yayin da suka samu damar tserewa sakamakon sakacin jami’an mu. Har yanzu akwai mutane 28 da suka tsere basu dawo ba.” Inji Jafaru.

Yan fursuna sun tarwatsa gidan Yari, sun fantsama cikin gari
Yan fursuna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jafaru Ahmed ya koka inda yake cewa da dama daga cikin mutanen da suka tsere yan fashi ne da kuma masu garkuwa da mutane, bugu da kari babban jami’in yace zasu cigaba da farautar mutanen, don ganin sun tabbatar da tsaron mutanen garin.

Daga karshe babban kwantrolan ya musanta batun da ake yayatawa na cewa wai matsalar ta faru ne sakamakon cin zarafin mazauna gidan yarin da jami’an ke yi, inda yace sun shirya hakan ne don yanta kan su ba a kan ka’ida ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng