Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga

Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga

- A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa wasu matasa da ke zanga-zanga sun balle gidan yari a Benin, jihar Edo

- Rundunar 'yan sanda ta ce ba za ta lamunci tashin hankali ba ganin yadda aka samu gurbatattu a cikin masu zanga zangar ENDSARS

- Ana zargin ma su zanga-zanga da tafka barna, su kuma ma su zanga-zanga na zargin an yi hayar batagari don su bata musu zanga-zanga

Hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo.

Legit.ng Hausa ta rawaito yadda wasu batagarin matasa su ka balle wani gidan yari da ke kan titin Sapele a birnin Benin da safiyar ranar Litinin.

Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Edo ta sanar da saka dokar ta baci ta sa'a 24.

A cikin wani jawabi da NCS ta fitar ranar Talata ta hannun darektan yada labarai da hulda da jama'a, Mohammed Manga, hukumar ta bayyana cewa ''ma fi yawan ma su laifin da su ka tsere wadanda ke jiran mutuwa ne bayan an yanke mu su hukunci kisa.

KARANTA: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga

Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga
Ma su zanga-zanga
Asali: Original

"Ma su zanga-zanga a karkashin tutar ENDSARS sun kai hari kan wasu gidajen yari biyu; daya a birnin Benin, daya a Oko, a jihar Benin tare da sakin fursuna 1,993 tare da lalata kayayyaki da suka hada da makaman da ke ajiye a dakin adanasu.

KARANTA: Na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo

"Matasan na da yawan gaske, sannan su na dauke da makamai ma su hatsari. Ba su boye niyyarsu ta balle dakuna domin sakin ma su laifi ba, kuma sun aikata hakan bayan sun zane jami'anmu da ke kan aiki a lokacin.

"Sakin ma su laifin hatsari ne ga tsaron kasa, lafiya da dukiyoyin jama'a. Ba za mu yarda da irin wannan hali ba, tuni mun fara bincike domin gano dukkan barnar da aka tafka yayin harin da aka kai gidajen yarin" a cewar jawabin.

Jawabin ya kara da cewa NCS ta tsaro a dukkan gidajen yari da ke fadin kasa tare da fara bin diddigin dukkan fursunonin da su ka tsere.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel