Kano: Bashir Ahmed da Aisha Yesufu Sun Buga Kan Matakin Abba Kabir Game da Haramta Fim

Kano: Bashir Ahmed da Aisha Yesufu Sun Buga Kan Matakin Abba Kabir Game da Haramta Fim

  • Hadimin, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya soki Aisha Yesufu bayan ta caccaki Gwamna Abba Kabir
  • Aisha ta soki gwamna bayan haramta fina-finan 'yan daudu yayin da ta ke martani kan fitaccen dan daudu, Idris Bobrisky
  • Bashir ya nuna goyon bayansa kan matakin da Gwamna Abba Kabir ya dauka inda ya ce su na goyon bayan dakile matsalar a Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya fina-finai da ke dauke da 'yan daudu, an fara cece-kuce a kai.

Fitacciyar mai fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu ta yi martani mai zafi a shafin x kan matakin yayin da ta ke martani kan ɗan daudu, Idris Bobrisky.

Kara karanta wannan

Bayan Kaduna, Gwamnan APC ya zargi uban gidansa da yashe lalitar gwamnati gaba ɗaya

An kai ruwa rana da Bashir Ahmad da Aisha Yesufu kan matakin Abba Kabir
Bashir Ahmad ya soki Aisha Yesufu kan caccakar Abba Kabir na Kano. Hoto: @AishaYesufu, @Kyusufabba, @BashirAhmaad.
Asali: Twitter

Aisha Yesufu a kan 'yan daudu a Kano?

Yesufu ta ce tun kafin Bobrisky ya yi suna, jihar Kano ke da 'yan daudu shekaru da dama da suka wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan daudu sun daɗe su na yawo a Kano tun kafin Bobrisky ya yi suna, har yanzu Bobrisky akwai abubuwan da ya kamata ya koya a Kano wadanda ba sai sun yi tiyata domin su sauya ba."
"Ku ci gaba da munafurcinku wurin mayar da shi wani abin daban."

- Aisha Yesufu

Martanin Bashir Ahmad ga Aisha Yesufu

A martaninsa, tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kakkusar suka ga Aisha kan wannan martani nata a shafinsa na X.

Ahmad ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan wannan mataki da ya dauka na haramta fina-finan 'yan daudu.

"Ko da kuwa akwai daudu a Kano fiye da shekaru dubu, meye abin ta da jijiyoyin wuya domin gwamnatin Kano ta na son kawo gyara yanzu?."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Bobrisky a Legas

"Koma dai waye ya shafa, abu ne marar kyau gaba daya wanda ya sabawa addininmu da kuma al'adunmu."
"Muna tare da Gwamna Abba Kabir kan wannan mataki da ya dauka domin kawar da matsalar gaba daya."

- Bashir Ahmad

Abba Kabir ya haramta fim din 'yan daudu

A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya ba da sabon umarni ga masu shirya fina-finai a masana'antar Kannywood a Kano.

Gwamnan ya haramta shirya fina-finai da suka shafi na 'yan daudu da kuma ayyukan 'yan daba a jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel