Musulmai Na Murna Yayin da Gwamna Kirista Ya Biya Cikon Kudin Kujerun Hajji Ga Maniyyata

Musulmai Na Murna Yayin da Gwamna Kirista Ya Biya Cikon Kudin Kujerun Hajji Ga Maniyyata

  • Yayin da ake ta korafi kan karin kudin kudin hajji, gwamnan jihar Ribas ya biyan cikin kudin da ake nema
  • Siminalayi Fubara ya biya wa maniyyata a jihar 41 cikon kudin N1.9m da hukumar alhazai ta sanar da karin
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani maniyyaci da kuma wanda ya riga ya gudanar da aikin hajji a shekarar bara kan karin kudin kujerun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya dauki nauyin biyan cikin kudin hajji ga maniyyata a jihar.

Fubara ya biya cikon kuɗin kujerun ne bayan karin kudi da hukumar alhazai ta yi, cewar Politics Digest.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamnan PDP ya biya rabin kuɗin da aka ƙarawa mahajjatan jihar Arewa, ya faɗi dalili

Gwamna Kirista ya daukewa alhazai nauyin biyan cikon kudin kujerar hajjj
Gwamna Siminalayi Fubara ya biya cikon kudin kujerar hajjj ga maniyyatan Ribas. Hoto: Siminalayi Fubara, NAHCON.
Asali: Facebook

Matakin da gwamnan ya dauka ga maniyyata

Wani daga cikin maniyyatan a jihar, Alhaji Yakubu Aliyu shi ya bayyana haka ga jaridar BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yakubu ya na daga cikin shugabannin 'yan Arewacin Najeriya da ke zaune a jihar ta Ribas a Kudancin ƙasar.

Ya ce gwamnan ya biya cikon kudin kujeru 41 a jihar na N1.9m da hukumar alhazai ta kara.

Martanin maniyyaci a Ribas kan lamarin

"Gwamnan ya biya cikon kudi da ake nema na kujeru 41 har N1.9m, daman gaba daya aka saye su, sannan ya kara siyan kujeru 6 a kan kuɗi N8m."
"Jimillan kujerun ya kai 47 kenan wanda aka ba Musulmai da ke jihar Ribas wadanda Allah ya ci da su."
"Daman kujeru 34 aka warewa jihar Ribas amma gwamnan sai da ya yi kokarin samun karin kujerun zuwa 47 domin a samu da yawa."

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya da suka ba alhazai tallafin kudin aikin Hajji

- Yakubu Aliyu

Musabbabin karin da hukumar alhazai ta yi

Wannan na zuwa ne bayan hukumar alhazai ta kara kudin kowace kujera da kan kuɗi N1.9m ga maniyyatan kasar.

Hukumar ta ce karin ya zama dole ganin yadda farashin dala ke kara tashi a fadin kasar baki daya da sauran sauye-sauye a hukumar.

Karin kudin ya shafi maniyyata da dama

Legit Hausa ta ji ta bakin wani maniyyaci da kuma wanda ya riga ya gudanar da aikin hajji a shekarar bara kan karin kudin kujerun.

Manu Abdulkadir da ke Gombe ya ce shi ya riga ya cire ransa tuntuni kan sauke farali, daman ya yi niyyar siyar da shanunsa ne amma bai samu ba.

“Tun bayan kara kudin nasani zai yi wahala na samu ikon zuwa saboda kudinmu kadara ne daman.”
“Amma dai kamar yadda sauran gwamnoni ke saka tallafi har yanzu babu wani labari daga jihar Gombe.'

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

- Manu Abdulkadir

Alhaji Kabiru Yawale daga karamar hukumar Biu a jihar Borno ya ce ya ziyarci kasa mai tsarki a 2022 inda ya ce tabbas karin ya shafi maniyyata da dama saboda yawansu ya ragu a karamar hukuma da kuma jihar.

"Karin ya shafi mafi yawan maniyyata a jihar Borno, gaskiya a Borno kam babu labarin tallafi daga gwamnati, amma muna saka rai gwamnanmu mai tausayi ne zai yi wani abu."
"Mafi yawan maniyyata da suke kusa da ni ba za su iya biya ba daman a Biu mutum dari da kadan ne suka biya, amma labarin da muke samu bai wuce mutum 18 ba ne suka cika kudinsu."

- Kabiru Yawale

Abba Kabir ya agazawa maniyyatan Kano

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki alƙawarin biyan wani kaso na cikon kudin aikin hajji.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne bayan hukumar alhazai ta kara kudin kujera da karin N1.9m ga kowace kujera daya a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel