Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Dalilansu Na Zuwa Amurka Taron Zaman Lafiya

Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Dalilansu Na Zuwa Amurka Taron Zaman Lafiya

  • Gwamnonin jihohin Arewa sun bayyana dalilansu na zuwa har kasar Amurka domin gudanar da taro a kan zaman lafiya
  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ne ya bayyana dalilan a madadin sauran gwamnonin yayin da ake sukarsu
  • Bayan kammala taron, gwamnonin kasar sun yi godiya ga Amurka tare da mika kokon bara domin cimma buri guda daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi bayani a kan dalilin zuwan wasu daga cikin gwamnonin Arewa taron zaman lafiya a Amurka.

Dr Dikko Radda
Matsalar tsaro ta sa gwamnonin Arewa zuwa Amurka neman mafita. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Taron wanda ya gudana na tsawon kwanaki uku, daga 23 zuwa 25 ga watan Afrilu, an yi shi ne a cibiyar zaman lafiya ta Amurka (USIP).

Kara karanta wannan

"Ku daina tsoma baki a gwamnatina" Gwamna ya gargaɗi tsofaffin gwamnoni

Dalilin zuwan gwamnonin Arewa Amurka

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa gwamnoni 10 ne daga Arewa ta tsakiya da Arewa ta yamma suka samu halartar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce sun fiskanci kalubale wurin masu ganin bai da ce a je Amurka tattauna matsalar ba.

Amma a cewarsa fita waje a yi musayar ra'ayoyi abu ne mai matukar muhimmanci wurin shawo kan matsaloli.

Gwamnan ya kara da cewa lalle fita zuwa wasu kasashe domin haduwa da mutane masu hikimomi daban-daban abin a yaba ne musamman lura da yadda duniya ta dunkule wuri guda.

Wata bukatar da gwamnonin suka nema

Gwamna Radda ya kara neman cigaban goyon baya da haɗaka wurin dakile matsalolin Arewa tsakanin gwamnonin da gwamnatin Amurka, cewar jaridar Daily Post

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

Radda ya kuma ce a madadin dukkan gwamnonin da suka halarci taron suna fatan sake samun irin damar domin tattaunawa a kan matsalolin da suka shafi yankin Arewa.

Matsalar ruwa ta kawo wahala a Arewa

A wani rahoton kuma, kun ji cewa matsalar ruwa ta addabi garuruwa kamar Gombe, Kano, Yobe da makamantansu a Arewacin Najeriya

Matsalar da ta haɗa da tsadar ruwan da rashin samunsa ta fara kawo tsaiko a cikin harkokin addini, sha'anin rayuwa da kiwon lafiya.

Bincike ya tabbatar da cewa matsalar na da alaka mai karfi da cire tallafin wutar lantarki, lalacewar wutar da karin kudin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel