Dubu Ta Cika: An Kama Matashin da Ya Haɗa Baki da Wasu Suka Yi Barazanar Sace Kawunsa

Dubu Ta Cika: An Kama Matashin da Ya Haɗa Baki da Wasu Suka Yi Barazanar Sace Kawunsa

  • Yan sanda sun kama mutum uku bayan sun karbi kuɗin fansa N2m daga kawun ɗaya daga cikinsu a jihar Nasarawa
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce waɗanda ake zargin sun yi wa kawun barazanar sace shi ko ya biya N2m
  • Dukkan mutanen sun amsa laifin da ake zarginsu yayin da ƴan sanda ke ci gaba da neman ragowar ɗan tawagarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wani mutum da laifin hada baki da wasu mutane biyu domin yin garkuwa da kawunsa.

Kamar yadda Leadership ta rahoto, mutumin da abokan da ya haɗa baki da su sun nemi kawunsa ya biya fansar N2m ko kuma su yi garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

Dangin amarya sun nuna jarumta, sun afkawa yan bindiga yayin da suka tare su a Zamfara

Yan sanda.
Yan sanda sun kama mutum uku yayin karɓan kudin fansa a jihar Nasarawa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun kama mutane

Jami’an rundunar ‘yan sandan da ke yankin Mararaba ‘A’ a karamar hukumar Karu ne suka kama mutanen uku bayan sun karɓi kuɗin N2m cas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Lafiya.

Ya jero sunayen waɗanda ake zargin da suka haɗa da Babangida Abdullahi, Mohammed Abubakar da Yakubu Sani, dukkansu mazauna Aso B Mararaba ne a yankin Karu.

Yadda suka karbi kudin fansar N2m

Nansel ya ce wadanda ake zargin sun yi wa Ibrahim Idris, kawu ga daya daga cikinsu barazanar ya ba su N2,000,000.00 ko kuma a yi garkuwa da shi.

Kakakin ƴan sandan ya ce saboda tsorata da barazanarsu, kawun ya haɗa kuɗi ya kai wurin da suka faɗa masa, daga nan aka kama su suna tsaka da raba kuɗin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun baƙunci lahira a hanyar zuwa kai hari kan mutane a jihar Borno

“Sun yi barazanar sace shi idan bai biya kudin fansar Naira miliyan biyu ba. Saboda tsoron a yi garkuwa da shi, ya kai masu kudaden da suka nema, bayan sun karba suka raba a tsakaninsu.
"Wadanda ake zargin duk sun amsa laifin, kuma ana ci gaba da kokarin cafke wani dan tawagarsu da ya tsallake rijiya da baya yayin da ƴan sanda suka je kama su."

- DSP Ramhan Nansel.

Dangin amarya sun daƙile harin 'yan bindiga

A wani rahoton na daban, an ji dangin amarya da fasinjoji sun nuna jarumta yayin da suka afkawa ƴan bindigar da suka tare su a titin Talatan Mafara zuwa Gusau

Rahoto ya nuna cewa sun yi nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindigar na sace amarya kuma sun kashe ɗaya daga cikin ƴan ta'addan

Asali: Legit.ng

Online view pixel