Kano: Mai POS Ya Maida N10m Bayan Kwastomansa Ya Tafka Kuskure, Ya Samu Kyauta
- Wani mai sana'ar POS a jihar Kano ya yi abin alheri bayan mayar da Naira miliyan 10 da aka tura masa bisa kuskure
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da hakan inda ta ce wani dan kasuwa ya yi kuskuren tura miliyan 10 madadin N10,000 ga mai POS din
- Mai POS din mai suna Muhammad Sani Abdulrahman ya kai rahoton ofishin 'yan sanda ne tun a watan Disambar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yabawa wani mai sana'ar POS da abin kirki da ya yi.
Mai sana’ar POS din ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa.
Kuskuren tura Naira miliyan 10 a POS
Hakan ya faru ne yayin da kwastoman ke kokarin tura N10,000 amma ya yi kuskuren tura miliyan 10.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar 'yan sanda ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, Abdullahi Haruna Kiyawa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 14 ga watan Maris.
Kiyawa ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a watan Disambar shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS, Mohammed Sani Abdulrahman ya kawo rahoto ofishinsu.
Ya ce Abdulrahman ya fahimci kwastomansa ya yi kuskuren tura masa Naira miliyan 10 madadin N10,000.
Daga nan ne rundunar ta karbi bayanan abin da ya faru tare da fara gudanar da bincike domin tabbatar an samu mai shi.
Tsawon lokacin da aka dauka ana bincike
Rundunar ta ce ta shafe watanni uku ta na bincike kafin ta gano mai kudin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.
Kiyawa ya ce mai POS ya mayarwa mai kudin hakkinsa inda ya ba mai POS ɗin kyautar N500,000.
Har ila yau, rundunar 'yan sandan ta yaba da kyakkyawan halin da mai POS din ya nuna kuma ta shawarci sauran jama’a da su yi koyi da shi.
Wannan ma zuwa ne bayan wani mai adaidaita sahu ya mayar da miliyan 15 ga wani kwastoman dan kasar Chadi a Kano.
Izala ta karrama dan agaji
Kun ji cewa Kungiyar Izala ta karrama dan agaji da ya tsinci kudi tare da mayarwa mai shi a jihar Katsina.
Matashin mai suna Salisu Abdullahi ya tsinci miliyan 100 a jihar Katsina inda ya mayarwa mai shi.
Asali: Legit.ng