‘Dan Agaji Ya Mayar da Kudi Naira Miliyan 100 da Ya Tsinta, An Yi Masa Kyaututtukan Ban Mamaki

‘Dan Agaji Ya Mayar da Kudi Naira Miliyan 100 da Ya Tsinta, An Yi Masa Kyaututtukan Ban Mamaki

  • Salihu Abdulhadi Kankia, wani ‘dan kungiyar Musulunci ta JIBWIS da ke jihar Katsina, ya tsinci jakar kudi
  • Matashin ya mayar da jakar da ke dauke da kudi sama da naira miliyan 100 ga mai ita ba tare da ya dauki ko kwabo ba
  • Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin kasa na zamani, Ali Pantami ya jinjinawa Kankia a shafinsa na soshiyal midiya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Fitaccen malamin Musulunci kuma tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin kasa na zamani, Sheikh Ali Isa Pantami, ya yi jinjina ga wani matashi ‘dan kungiyar JIBWIS, Salihu Abdulhadi Kankia.

Abdulhadi Kankia wanda ya fito daga jihar Katsina, ya tsinci wata jaka dauke da kudi sama da naira miliyan 100.

Kara karanta wannan

'Dan gida ya fasa kwai, ya jefi Gwamnatin Tinubu da biyewa manufofin turawa

Salihu Abdulhadi Kankia
‘Dan Agaji Ya Mayar da Kudi Naira Miliyan 100 da Ya Tsinta, An Yi Masa Kyaututtukan Ban Mamaki Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Sai dai kuma, matashin ya mayar da jakar ga mai ita ba tare da ya cire ko sisin kwabo a ciki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An karrama matashin da ya tsinci miliyan 100

Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, ya karrama matashin saboda gaskiyarsa, inda ya ba shi lambar girmamawa da kuma kujerar aikin hajji.

Haka kuma, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ba shi kyautar mota yayin da wani ‘dan majalisar wakilai ya yi masa kyautar kudi naira miliyan biyu.

Da yake yada labarin a shafinsa na X, Pantami ya bayyana cewa matashin ya daga darajar kansa da ta iyayensa sakamakon gaskiya, mutunci da amana da ya nuna.

Haka kuma, Pantami ya yi kira ga duk wanda zai iya daukar nauyin karatun yaron koda zuwa matakin digiri ne da ya tuntubi iyayensa domin yin tsare-tsaren da ya dace kan haka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dura kan 'yan Crypto, ta kakaba wa Binance tarar dala biliyan 10

Jama'a sun yi martani

@MAbba_FX:

"Masha Allah."

@Nasir1on1 ya ce:

"Ameen. Tabarakallah masha Allah."

@RMaitano ya ce:

"Masha Allah ! Allah ya Kara taimakon shi Ameen ya Allah ."

@King_bosskidz ya ce:

"Kai amma yaron nan jaki ne wlh."

@ekeree44:

"Allahu Akbar , Allah yabada Lada.
"Dadin danakeji har araina shine salihu daga garina ya hito . @MSIngawa kazohwa malam na magana."

'Yar bautar kasa ta mayar da wayar da ta tsinta

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa hukumar NYSC ta yaba ma wata 'yar bautar kasa, Adedeji Taofeekat Adebimpe, wacce ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max sannan ta mika shi ga mahukunta don mayar da shi ga mai ita.

Hukumar NYSC ta bayyana hakan a shafinta na X a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel