Kungiyar Musulunci Ta Tsoma Baki, Ta ce Mutumin da Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu Ya Canza Tunani

Kungiyar Musulunci Ta Tsoma Baki, Ta ce Mutumin da Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu Ya Canza Tunani

  • Kungiyar MURIC ta yi karin haske kan mutumin Sokoto da ya nemi a kashe matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu
  • MURIC mai kare hakkin Musulmi ta ce Sanusi Abubakar wanda ya boye karkashin sunan malami ya janye kalaman da ya yi kan matar shugaban kasar
  • Ta ce Abubakar ya kuma bayar da hakuri cikin wasikar da ya rubuta yana mai tabbatar da kalamansa baya bisa tsarin koyarwar Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Sokoto -Wani mutumi da ya nemi a kashe matar Shugaban kasa, Remi Tinubu, saboda addininta ya janye kalamansa sannan ya nemi afuwa.

Sanusi Abubakar ya ce ya yi furucin ne a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, domin nemawa jam’iyyarsa goyon baya, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiya a Arewa ta fadi abin da ya kamata Tinubu ya yi wa malamin da ya zagi matarsa, ta fadi dalili

Mutumin da ya nemi a kashe matar shugaban kasa ya janye kalamansa
Kungiyar Musulunci Ta Tsoma Baki, Ta ce Mutumin da Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu Ya Canza Tunani Hoto: Sen. Oluremi Tinubu, CON
Asali: Facebook

Mista Abubakar, wanda ke zaune a jihar Sokoto, ya janye kalaman nasa ne bayan ya tuntubi kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Hassan Indabawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Mun nesanta kansu daga kalamansa, MURIC

Ya ce hedkwatar MURIC ta yi Allah wadai dannan ta nesanta kanta da kalaman mutumin a ranar Juma’ar da ya yi maganar.

Indabawa ya ce:

“Da yake martani ga sanarwar da MURIC ta saki a ranar Juma’a, 23 ga watan Fabrairun 2024, wani mutum mai suna Sanusi Abubakar wanda ya badda kammani a matsayin malamin Musulunci, ya tuntunbi MURIC,.
"Yana mai janye duk wasu kalamansa na rashin tunani, tsokana, ganganci da bata da ya yi na kira da a kashe Sanata Remi Tinubu, uwargidan shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

Atiku ya karantar da Tinubu, ya fadawa Shugaban kasa hanyar gyara a saukake

Abubakar ya yarda a wasikar ban hakurinsa cewa furucinsa baya bisa tsarin koyarwar addinin Musulunci, rahoton The Cable.

A halin da ake ciki, Indabawa ya ce kungiyar MURIC ta yi kira da a samar da ka’idojin wa’azin addini don magance kalaman kiyayya da wasu malamai ke yi.

Anyi tir da mutumin da ya nemi kashe matar Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi martani bayan wani malamin addinin Musulunci ya ayyana cewa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta cancanci mutuwa saboda kasancewarta fasto.

Sani ya yi Allah wadai da furucin malamin sannan ya jaddada cewar 'yan kasa na da 'yancin sukar gwamnati da manufofinta, amma neman mutuwar matar shugaban kasar ba abun yarda bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel