Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

An sa matan Arewa da tsantsar kyawu wanda da zaran ka daura idanu a kansu bazaka iya hakuri ba sai ka kara kallonsu karo na biyu.

Allah ya albarkaci ‘ya’yan biloniyan arewacin Najeriya da irin wannan tsantsar kyawun.

Bayan Allah ya albarkace su da kyawu, sun kasance masu aji sannan kuma daga tsatson arziki.

Da yawa a cikinsu basa daukar kansu da zafi, duk da cewan an haife su cikin daula da matsayi.

Kalli hotunan kyawawan ‘ya’yan wasu daga cikin miloniyan guda 10.

1. Adama, Mairama da kuma Meram Indimi:

Sun kasance ‘yaya attajirin dan kasuwa kuma biloniya Mohammed Indimi, shugaban kamfanin Oriental Energy Resouces, daya daga cikin manyan kamfanonin da ake samar da mai a Najeriya.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

2. Gimbiya Hadiza Idris:

Wannan kyakkyawar matashiyar ta kasance ya ga sarkin Zazzau, Alhaji (Dr) Shehu Idris a Zaria. Kuma mata ga Jibrilla, dan attajirin dan kasuwa kuma biloniya, Mohammed a Zaria, jihar Kaduna.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

3. Zahra da Halima Buhari:

Sun kasance ‘ya’yan shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

4. Zainab Yari

Ta kasance kyakyawar yarinyar gwamnan jihar Zamfara, Abdula’aziz Abubakar Yari.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

5. Walida, Aisha da kuma Asmau Atiku:

sun kasance ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Duk sunyi aure a rana daya, ranar 13 ga watan Nuwamba, 2015.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

6. Aisha Dangiwa Umar:

Wannan fara kyakkyawar ta kasance yar tsohon gwamnan jihar Kaduna a mulkin soja. Tana auren dan tsohon gwamnan jihar Kebbi Mustapha Adamu Aliero.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

7. Halima, Fatima da Sadia Dangote:

Sun kasance ‘ya’yan biloniya dan Najeriya kuma daya daga cikin masu kudin duniya, Aliko Dangote.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

8. Shahida da Siddika Sanusi:

Sun kasance ‘ya’yan tsohon shugaban babban bankin Najeriya, wanda a yanzu shine sarkin Kano, Muhammad Sauni II.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

9. Aisha Badaru:

Wannan kyakkyawar ta kasance yar gwamna Alhaji Mohammed Abubakar Badaru na jihar Jigawa.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

10. Bara’atu Muazu:

Ta kasance ‘ya ga Adamu Muazu, tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa.

Hadaddun hotuna 10 na kyawawan ‘ya’yan masu kudin Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel