Atiku Ya Karantar da Tinubu, Ya Fadawa Shugaban Kasa Hanyar Gyara a Saukake

Atiku Ya Karantar da Tinubu, Ya Fadawa Shugaban Kasa Hanyar Gyara a Saukake

  • Atiku Abubakar ya yabi salon mulkin Javier Milei wanda ya karbi shugabancin kasar Argentina a karshen shekarar 2023
  • Wazirin Adamawa ya ce matsalolin Argentina da Najeriya kusan iri daya ne, amma dabarun shugabannin sun bambanta
  • Atiku ya kawo shawarar koyi da gwamnatin Milei wajen rage facaka, a saida kadarorin gwamnati kuma a tuna da matasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Atiku Abubakar wanda ya rikewa PDP tuta a zaben shugaban kasa na 2023, ya sake yin magana a kan tattalin arzikin Najeriya.

Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da wani dogon sako zuwa ga Bola Ahmed Tinubu a dandalin X, ya ba gwamnatin tarayya shawarwari.

Atiku
Atiku yana so Tinubu ya yi koyi da Shugaban Kasar Argentina Hoto: Luis Robayo Source: Getty Images
Asali: Getty Images

‘Dan takaran kuma babban jigo na jam’iyyar PDP ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu tayi koyi da salon shugaba Javier Milei a Argentina.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku na ba shi shawara kan tattalin arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya kawo mafita ne ganin Najeriya ta shiga kunci da matsin lambar tattalin arziki.

Gwamnatocin Milei da Tinubu

Jagoran adawar yake cewa kasashen Najeriya da Argentina sun samu kansu a mummunan yanayi, kowa ya kawo hanyar gyara.

Halin da Javier Milei ya tsinci kasar Argentina, a cewar Wazirin Adamawa ya fi muni a kan yadda Muhammadu Buhari ya mika mulki.

Daga kalamansa a X, Atiku yana ganin idan Tinubu ya yi koyi da gwamnatin Milei, tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa, a samu arziki.

Zargin ‘yan adawa ko daura laifi ga magabatansa ba mafita ba ne, Atiku ya fadawa gwamnati babu ruwan ‘yan kasuwa da siyasar gida.

Tinubu: Maganar Atiku a kan Argentina

"Matsalolin Argentina na kama da Najeriya – hauhawar farashin kaya, talauci da tulin bashi, Milei yana shiga ofis, ya rage facaka."

Kara karanta wannan

Matakin Tinubu 1 ya jefa Najeriya cikin wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

"Ya fara da rage batar da kudi a gwamnati; ya toshe hanyoyin sata, ya jawo masu hannun jari ta hanyar cire haraji da saukaka kasuwanci."
"Idan zai yi tafiya, Milei yana yankan karamar kujera ne a jirgi, ba a amfani da jirgin shugaban kasa waje bikin ranar haihuwar yaronsa."
"Milei bai kafa gwamnatin da ta fi kowace girma kamar yadda Tinubu ya yi a lokacin da tattalin arzikin kasarmu yake a durkushe ba."

- Atiku Abubakar

Atiku ya jero bambancin Tinubu da Milei

A yayin da Tinubu ya kara Ministoci, shugaban Argentina ya rage adadin ma’aikatu ne.

Javier Milei ya yi gwanjon kadarorin gwamnatin kasarsa, shiyasa Alhaji Atiku ya ce tsare-tsarensa sun zo daidai da irin na sa a Najeriya.

Tibubu da cire tallafin fetur

Ana da labari cewa Babachir David Lawal ya zargi Bola Tinubu da nuna girman kai wajen cire tallafin man fetur daga hawa kan mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Injiniya Babachir ya ce bai dace a soke tsarin tallafin fetur ba tare da tare tuntubar kowa ba, wannan ya jefa kasar a halin wayyo Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel