An Shiga Jimami Bayan Mutane da Dama Sun Rasu a Wani Mummunan Hatsarin Mota

An Shiga Jimami Bayan Mutane da Dama Sun Rasu a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • Wani hatsarin mota da ya auku a jihar Ondo ya yi sanadiyyar fasinjoji mutum hudu bayan motarsu ta faɗa rami
  • Wasu mutum 10 kuma sun samu raunuka bayan motar bas ɗin ta ƙwace ta faɗa ciin ramin a safiyar ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu
  • Jami'ar hulɗa da jama'a ta ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar hatsarin ta ce an kai mutanen zuwa asibiti domin duba waɗanda suka samu raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Fasinjoji huɗu ne suka mutu yayin da wasu mutum 10 suka samu raunuka bayan da wata motar safa da ke cikin sauri ta afka cikin wani rami da ke Ore a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke rikakkun masu sace yara a Arewacin Najeriya, bayanai sun fito

Wani ganau ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 6:30 na safe inda direban bas ɗin, ta kamfanin Chisco mai lamba KSF 93 YG, ya rasa yadda zai yi, sannan ya shiga cikin ramin.

An yi hatsarin mota a jihar Ondo
Mutum hudu suk rasu a hatsarin mota a Ondo Hoto: FRSC Nigeria
Asali: Facebook

Shaidan wanda ya so a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust a ranar Lahadi cewa jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun yi gaggawar ziyartar wurin tare da jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa domin kwashe waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumomi suka ce kan hatsarin?

Da take tabbatar da faruwar hatsarin a cikin wata sanarwa, jami’ar hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ɗora alhakin aukuwar hatsarin kan direban motar bas ɗin, cewar rahoton Channels tv.

Odunlami-Omisanya ta bayyana cewa direban da ke tuƙa fasinjoji daga Port Harcourt zuwa jihar Legas ya rasa yadda zai yi da motar kafin hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

Bayin Allah da yawa sun mutu yayin da ƴan bindiga suka buɗe wa jama'a wuta a jihar Arewa

A kalamansa:

"Yan sanda sun garzaya da fasinjojin da ke cikin motar zuwa asibitin Grace of God. An tabbatar da mutuwar mutum huɗu inda aka ajiye gawarwakinsu a ɗakin ajiyar gawa na asibitin yayin da mutum 10 suka samu raunuka kuma suna samun kulawa.

Mota Ta Faɗa Kogi a Ogun

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mota faɗa cikin kogi bayan ta yi hatsari a kan gadar Iju ta da ke ƙaramar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun.

Hatsarin da ya auku ya haɗa da wata babbar mota, Keke Napep guda biyu da wata mota a kan gadar kogin Iju.

Asali: Legit.ng

Online view pixel