'Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun Masu Sace Yara a Arewacin Najeriya, Bayanai Sun Fito

'Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun Masu Sace Yara a Arewacin Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da cafke wasu miyagu da ake zargi da satar ƙananan yara suna sayarwa a kasuwa
  • Ƴan sandan sun cafke mutanen ne bayan an kama wani ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin sace wani ƙaramin yaro a Keffi
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da cafke miyagun, ya ce bincike ya nuna cewa sun daɗe suna aikata wannan mummunar ɗabi'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutum 10 bisa zargin satar yara da sayar da su.

Shehu Nadada, kwamishinan ƴan sandan jihar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke birnin Lafia a ranar Juma’a, cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a jihar Arewa

'Yan sanda sun sace masu sace yara a Nasarawa
'Yan sanda sun yi nasarar cafke masu satar kananan yara a Nasarawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan ya ce jami’an ƴan sandan da ke aiki da sashen Keffi, a sintiri na yau da kullum a ranar 10 ga watan Janairu, sun ceto wani mutum daga masu shirin yi masa taron dangi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke miyagun

Da aka gudanar da bincike, an gano cewa ana zargin mutumin da sace wani yaro ɗan shekara biyar a Keffi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Nadada ya ce daga baya wanda ake zargin ya amsa laifin cewa shi mamba ne na ƙungiyar da ta ƙware wajen satar yara da sayar da yara ga manyan ƴan kasuwa.

Ya ce binciken da aka yi ya kai ga kama wasu mambobin ƙungiyar mutum tara.

Ya ƙara da cewa binciken da aka yi a wayoyinsu ya nuna cewa sun yi awon gaba da yara 45 sun sayar da su, waɗanda aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki a jihar Arewa, sun halaka mutum 7 da sace wasu da dama

Ko da yake kwamishinan bai bayyana lokacin da aka sace yaran ba, ya ce yawancinsu an sace su ne daga jihohin Abuja, Kaduna, Nasarawa, Plateau da Neja.

Ya ce an ƙwato shida daga cikin yaran daga jihohin Abuja, Ondo da kuma Legas, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama wasu da ke da hannu a ciki tare da ƙwato sauran yaran.

Wanda ake zargin ya amsa laifin sayar da yaran a kan farashi daban-daban, tsakanin Naira 350,000 zuwa Naira miliyan 1.5 ya danganta da shekarunsu da jinsinsu.

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Ɗan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda a jihar Sokoto sun samu nasarar sheƙe wani ɗan bindiga a yayin wani artabu a jihar.

Jami'an ƴan sandan sun kuma cafke wasu mutum 15 a yayin artabun tare da ƙwato motocin da ƴan bindigan suke amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel