An Shiga Jimami Bayan Wata Mota Ta Fada Cikin Kogi, FRSC Fitar da Karin Bayani

An Shiga Jimami Bayan Wata Mota Ta Fada Cikin Kogi, FRSC Fitar da Karin Bayani

  • Wata mota da ta yi hatsari a kan gadar Iju da ke jihar Ogun ta faɗa cikin kogin, lamarin da ya yi sanadin toshe hanyar Ota-Idiroko gaba ɗaya
  • Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta bayar da sanarwar afkuwar lamarin tare da tura jami’anta domin gudanar da aikin ceto
  • Kakakin hukumar ta FRSC ta bayyana cewa, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kawar da toshewar tare da kula da harkokin ababen hawa a kan hanyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Wata mota da ta yi hatsari a kan gadar Iju ta faɗa cikin kogin, lamarin da ya yi sanadin toshe hanyar Ota-Idiroko da ke ƙaramar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

An bayyana hakan ne a cikin sanarwar da hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun ta fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu.

Hatsarin mota ya auku a Ogun
Wata mota ta fada.cikin kogi a wani hatsari a jihar Ogun Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, hatsarin da ya auku ya haɗa da wata babbar mota, Keke Napep guda biyu da wata mota a kan gadar kogin Iju.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an FRSC sun fara aikin ceto

Jami’an hukumar FRSC da sauran jami’an tsaro sun isa wurin da hatsarin ya afku domin shawo kan lamarin, cewar rahoton Tori.ng

Haka kuma an ce jami’an hukumar ta FRSC suna jiran isowar wata babbar mota domin gudanar da aikin ceton.

Kakakin Rundunar FRSC reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce ana kuma ƙoƙarin ciro motar daga cikin kogin.

A kalamanta:

"Hatsarin ya faru ne a gadar Iju dake kan titin Otta/Idiroko. Ya ritsa da babbar mota, Keke Napep guda biyu da kuma wata mota ƙirar Camry.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke babban malamin addini a Najeriya, ta fadi laifinsa

"An toshe hanyar Otta-Idiroko gaba ɗaya, jami'an tsaro suna nan suna kula da lamarin."

Mutum 6 Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar wani mummuman hatsarin mota.

A cewar hukumar hatsarin wanda ya auku a kwanar Onueke a hanyar Afikpo zuwa Abakaliki, ya salwantar da ran mutum shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel