Hukumar Hisbah a Kano Ta Kama Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya

Hukumar Hisbah a Kano Ta Kama Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya

  • Jami'an hukumar Hisbah masu tabbatar da tarbiya a jihar Kano sun kama fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya
  • An kama Murja ne bayan an shafe tsawon lokaci ana yi mata nasiha kan yada bidiyo na rashin tarbiya ba tare da ta ji ba
  • Hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ibrahim, ne ya sanar da batun kamun nata a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano karkashin jagorancin, Sheikh Aminu Daurawa, ta kama fitacciyar jarumar nan mai amfani da manhajar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.

Labarin kamun Murna na 'kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @babarh_.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Hisbah ta kama Murja Kunya
Hukumar Hisbah a Kano Ta Kama Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya Hoto: Murjanatu Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

Me yasa aka kama Murja?

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa an kama jarumar ne bayan an sha yi mata nasiha ba tare da ta sauya halinta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murja dai tana cikin shahararrun 'yan Tiktok guda shida da hukumar ta Hisbah ta sanar da nemansu ruwa a jallo.

Ana dai zarginsu da furta kalaman rashin tarbiya a bidiyon da suke yadawa, wanda hakan ya saba dokar tabbatar da tarbiya.

Ba wannan bane karo na farko da hukumar ke zaunar da Murja domin yi mata nasiha don ganin ta zama mutuniyar kwarai wacce za a yi alfahari da ita a cikin al'umma.

A kan haka ne ma, aka rahoto a baya cewa hukumar Hisbah za ta aurar da 'yar TikTok din a watannin baya, sai dai kuma har yanzu ba a kai ga haka ba.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar DSS ta tsare Sunusi Oscar kan wasu zarge-zarge, bayanai sun fito

Hadimin gwamnan ya rubuta:

"Bayan nasiha da jan hankali, hukumar Hisbah a jihar Kano, ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya."

Jama'a sun yi martani bayan Hisbah ta kama Murya Kunya

@Mr_stranger442 ya yi martani:

"Don Allah a Barta a nan har sai tayi tsatsa.
"Wannan yarinyar da sauran irin ta ba qaramar annoba bane a cikin al’umma."

@KhnSyf92414 ya yi martani:

"Gaskiya yakamata wan nan dai ayi mata wani babban hukun cin saboda yan baya don Gaskiya abun nata yana wuce gona da iri."

Murja ta aikewa Hisbah da sako

A baya mun ji cewa Murja Kunya ta maida martani yayin da aka ji ana nemanta.

Murja Kunya a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook tayi wa hukumar Hisbah raddi da cewa sun san inda ta ke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel