Hukumar Hisbah Na Neman Murja Kunya, Gfresh da Wasu Yan TikTok 4 a Kano, Ta Fadi Dalili

Hukumar Hisbah Na Neman Murja Kunya, Gfresh da Wasu Yan TikTok 4 a Kano, Ta Fadi Dalili

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da neman wasu shahararrun ƴan Tiktok guda shida a jihar
  • Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce ana nemansu kan kalaman batsa da suka yi a cikin wani bidiyo
  • Ƴan TikTok ɗin da hukumar ke nema sun haɗa da Sadiya Haruna, Gfresh, Murja Kunya, Hassan Makeup, Ummee Shakira da Ashiru Idris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da neman wasu shahararrun masu amfani da manhajar Tiktok guda shida.

Hukumar na neman mutanen ne saboda furta kalaman rashin ɗa'a cikin wasu bidiyo da suka yi, wanda hakan ya saɓa wa dokar tabbatar da tarbiyya.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa

Hisbah na neman yan TikTok a Kano
Hisbah na neman Murja Kunya da wasu yan TikTok a Kano Hoto: @yagamen1
Asali: TikTok

BBC Hausa ta kawo rahoto cewa shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa cikin ƴan TikTok ɗin da ake nema akwai Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gfresh.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da Sadiya Haruna, Ashiru Idris da aka fi sani da Maiwushirya, Ummee Shakira, Murja Ibrahim Kunya da Hassan Makeup.

Meyasa Hisbah ke nemansu?

A cewar shugaban na Hisbah, suna cigiyar ƴan TikTok ɗin ne bayan bayyanar wani bidiyo inda suke furta kalaman rashin tarbiyya a ciki.

Ya bayyana cewa kalaman na su, sun saɓa wa alƙawarin da aka ƙulla da su a karon farko da hukumar ta kama su domin yi musu wa'azi.

Sheikh Daurawa ya yi nuni da cewa tun da wannan ne karo na biyu da suke yi wa dokar karan tsaye, za a sake jan hankalinsu ne kawai kan rashin dacewar waɗannan ɗabi'un da suke yi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Yadda za a yi da su Murja

Ya kuma bayyana cewa za su tabbatar da cewa sun rubuta alƙawarin yin riƙo da yarjejeniyar da aka cimma da su.

Shugaban na Hisbah ya ce sai an yi wa doka hawan ƙawara sau uku sannan hukumar ke gurfanarwa a gaban kotu.

Hisbah Za Ta Aurar da Murja Kunya

A baya rahoto ya zo cewa hukumar Hisbah ta shirya aurar da jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya da sauran ƴan TikTok a jihar.

Shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya tabbatar da hakan, ya ce gwamnati za ta kuma ba su jari domin ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel