Kano: Hukumar DSS Ta Tsare Sunusi Oscar Kan Wasu Zarge-Zarge, Bayanai Sun Fito

Kano: Hukumar DSS Ta Tsare Sunusi Oscar Kan Wasu Zarge-Zarge, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta tsare daraktan fina-finan Kannywood, Sunusi Oscar kan zargin kalaman barazana
  • Ana zargin Oscar ne da furta kalaman a cikin wata murya da aka nada inda ya ke barazana ga wani jigo a gwamnati
  • Hukumar ta tsare Oscar ne a ofishinta da ke birnin Tarayya da ke Abuja inda aka masa tambayoyi kan kalaman

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tsare daraktan fina-finan Kannywood, Sunusi Oscar a Abuja.

Ana zargin Oscar da furta kalaman barzanar kisa a cikin wata murya da aka nada kan barazanar kisa.

DSS sun tsare Daraktan fina-finai tare da masa tambayoyi
Hukumar DSS ta tsare shi ne da zargin furta wasu kalamai marasa dadi. Hoto: Sunusi Oscar.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Oscar da aikatawa?

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya

Wata majiya ta tabbatar da cewa Oscar ya furta wasu kalaman barazanar kisa ga wani daga cikin gwamnatin jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminiya ta tabbatar da cewa tun farko an alakanta kama Oscar ne da shugaban hukumar tace fina-finai na Kano Abba EL-Mustapha.

Hakan ya biyo bayan rashin jituwar da ke tsakaninsu tun bayan darewar sabuwar Gwamnatin Kano ta NNPP kan karagar mulki.

Oscar ya godewa Kashim Shettima da sauran mutane

Rashin jituwar ta samo asali ne saboda kalaman da Oscar ya yi kan shugaban hukumar, inda yake cewa ya na jawo ’yan adawa jikinsa.

Sai dai wutar rigimar ta ci gaba da ruruwa bayan Oscar ya samu mukamin hadimin Gwamnan, inda ya ke yawan kaurace wa tarukan hukumar da kuma sukar shugabancin El-Mustapha.

Daga bisani, rahotanni sun tabbatar da sakin nashi inda ya wallafa a shafinsa na Facebook tare da yin godiya ga Ubangiji.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Oscar ya godewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Sanata Rufa'i Hanga da sauran mutane da dama.

Ya kuma godewa al'umma gaba daya da suka taya shi da addu'a da sauran kafafan yada labarai.

'Yan daba sun farmaki kwamishina a Adamawa

Kun ji cewa, wasu 'yan daba sun kai farmaki kan kwamishinan Muhalli a jihar Adamawa, Mohammed Sadiq a gidansa da ke birnin Yola.

Lamarin ya faru ne da daren jiya Lahadi 11 ga watan Faburairu inda kwamishinan ya samu raunuka a jikinsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka kwamishinan ya na kwance a asibiti mai zaman kansa da ke birnin Yola.

Asali: Legit.ng

Online view pixel