Hare-Haren 'Yan Bindiga: Shugaba Tinubu Ya Amince da Aiwatar da Wani Abu 1 a Jihar Arewa

Hare-Haren 'Yan Bindiga: Shugaba Tinubu Ya Amince da Aiwatar da Wani Abu 1 a Jihar Arewa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki kwakkwaran mataki domin kawo karshen matsalolin tsaro a jihar Filato
  • Shugaban Najeriyan ya amince da kafa wani sansanin sojoji saboda hare-haren da 'yan bindiga suka kai kananan hukumomin Bokkos, Mangu da Barkin Ladi
  • Kafa wannan sansani zai bayar da damar da sojoji za su dunga daukar matakan gaggawa domin dakile hare-haren 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Sakamakon hare-haren da ya yi sanadiyar rasa rayuka 200 a fadin kananan hukumomi uku a jihar Filato, da suka hada da Bokkos, Mangu da Barkin Ladi, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa sansanin sojoji.

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sansanin sojoji a jihar Filato
Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sansanin Sojoji a Jihar Arewa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa za'a kafa sansanin ne a Miller Farm (Gada Biyu) yankin Mbar da ke karamar hukumar Bokkos.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Wani tasiri kafa sansanin zai yi?

Shugaba Tinubu ya umurci Janar Christopher Musa, Shugaban ma'aikatan tsaro, da ya jagoranci aiwatar da wannan shiri domin magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, ya yi kokarin ganin an kafa sansanin soji don dakile hare-haren da ake ci gaba da kaiwa wanda ya haddasa asarar rayuka, da sace-sacen jama’a, da lalata dukiyoyi.

Da zarar an fara aiki, sansanin zai dunga kai matakan gaggawa don magance hare-hare da kashe-kashe a Bokkos, Mangu, Riyom, Barkin Ladi, da jihar Nasarawa mai makwabtaka, rahoton Allnews.

Wannan shiri yana da matukar muhimmanci musamman bayan korar wasu al’umma da aka yi tare da sace-sacen jama’a da kuma asarar rayuka a jajibirin Kirsimeti na 2023 a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, da Barkin Ladi.

Majalisa ta koka kan rashin tsaro a Abuja

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga 'yan Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa majalisar dattawan Najeriya, ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, ta nuna matuƙar damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a kasar nan.

Majalisar ta ayyana cewa babban birnin tarayya Abuja wurin da kujerar mulkin ƙasar take na fuskantar barazana, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce mahara sun kutsa cikin Abuja, inda ya kafa hujja da hare-haren da aka kai a wurare kamar Kubwa, Bwari da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel