Da Gaske Jami’an Tsaro Na Da Masaniyar ’Yan Ta’adda Za Su Kai Hari Jihar Filato? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske Jami’an Tsaro Na Da Masaniyar ’Yan Ta’adda Za Su Kai Hari Jihar Filato? Gaskiya Ta Bayyana

  • Biyo bayan wasu jerin munanan hare-hare a kananan hukumomin Filato, an gano cewa jami'an tsaro na da masaniyar kai harin
  • A cewar wani tsohon mataimakin sufeta janar na 'yan sanda, sun sanar da jami'an tsaro, amma ba su dauki mataki ba
  • Harin garuruwan Bakkos da Barkin Ladi a jihar Filato, ya yi silar mutuwar daruruwan mutane tare da asarar dukiya mai yawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Plateau - Tsohon mataimakin sufeta janar na 'yan sanda (AIG), Dabup Makama, ya ce jami'an tsaro na sane da za a kai hari Bokkos da Barkin Ladi a jihar Filato.

A cewar Makama, jami'an tsaro sun samu bayanan sirri na cewar za a iya kai harin, amma suka ki daukar mataki har aka kashe shi daruruwan mutane.

Kara karanta wannan

"Ba zama": Gwamnan jihar Arewa ya yi ganawar sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an gano dalili

kashe-kashe a Filato
Jami'an tsaro na da masaniyar za a kai hari jihar Filato amma suka ki daukar mataki - Tsohon AIG
Asali: Getty Images

Mun fadi wa jami'an tsaro za a kawo mana farmaki - Makama

Makama, wanda shi ne shugaban kungiyar 'Operation Rainbow' a jihar, ya dora laifin kai farmakin ga jami'an tsaron, inda ya ce sun gaza wajen kare rayukan jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata ne tsohon AIG Makama ya fitar da sanarwar, inda ya ce:

"Operation Rainbow' ya sanar da jami'an tsaro cewa za a iya kai farmaki a wasu garuruwa na jihar. Amma ba su dauki mataki ba, sun ja an kashe daruruwan mutanenmu."

Channels TV ta ruwaito Fatai Owoseni, babban mai ba gwamnan Oyo shawara kan tsaro, yana cewa akwai kuskuren jam'i'an tsaro a harin Filato.

Zuwan Kashim Shettima Filato don jajanta masu

Makama ya jinjinawa shugaba kasa Bola Tinubu kan tura Kashin Shettima da Nuhu Ribadu jihar Filato, don ganin irin barnar da 'yan ta'addan suka yi ma su.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

"Ya kamata Shugaba Tinubu ya sa a gudanar da tsattsauran bincike kan wannan hari, duk wanda ke da hannu a ciki a gaggauta kamo shi a hukunta shi."

A cewar Makama.

An kashe makiyayi a jihar Filato, jim kadan da kashe limami

A wani labarin, 'yan bindiga sun kashe wani Nuhu Adamu, wanda makiyayi ne da ke zaune a unguwar Mortal da ke Bakkos, jihar Filato.

Kisan makiyayin na zuwa kwanaki kadan da kashe wani limamin masallacin Juma'a, da kuma wani mai sana'ar acaba da aka yi a yankin Tangur da ke Bakkos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel