A Karon Farko, an Yi Bikin Nuna Ado a Saudiyya da Mata Suka Fitar da Cinyoyinsu Waje

A Karon Farko, an Yi Bikin Nuna Ado a Saudiyya da Mata Suka Fitar da Cinyoyinsu Waje

  • A kasar Saudiyya ne aka gudanar da wani bikin kwalliya da caba ado da nuna cinyoyi da kafadun mata
  • Wannan na daga cikin aikin da Yarima Muhammad Bin Salman ya dauko na sauya akalar takunkumi a kasar
  • Sai dai, ana ci gaba da cece-kuce daga bangarori daban-daban na duniya kan aikin da Yariman ya dauko

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Saudiyya - Wani yanayi mai daukar hankali ya auku a kasar Saudiyya, inda aka gudanar da bikin nuna ado na farko da ya nuna mata sanye da kayan ninkaya a jikinsu.

A bikin, an ga mata sanye da suturar da ke nuna kusan rabin tsiraicinsu, lamarin da ya dauki hankalin duniya.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

A biki, mata sun fito a bakin ramin ninkayan St Regis, inda suka yi dandazo tare da nuna irin surar da suke dashi kafin ninkayar.

Saudiyya ta sha bayyana aniyarta na tabbatar da saukaka kakaba al'adun turawa da wadanda ba Musulmai ba a kasar, rahoton Hindustan Times.

An yi bikin nuna ado a Saudiyya
Bikin nuna ado a Saudiyya ya jawo cece-kuce | Hoto: Hindustan Times
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana bikin casu a kasar Saudiyya

Wannan biki dai da aka yi an yi shi ne a daya daga cikin bukukuwan bude Red Sea Fashin Week da ake yi a filin wasannin St Regis da ke yammacin kasar.

A shekaru kasa da 10 da suka shude, doka ce a kasar Saudiyya cewa, dole mata suke sanya Hijabi ko Abaya kafin su fita waje, Arab News ta ruwaito.

Sai dai, a halin yanzu, Muhammad Bin Salman na kokarin tabbatar da kasar ta yi gogayya da dukkan kasashen duniya wajen nuna wayewa da iya cin duniya da tsinke.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta mayarwa Amurka $22,000 da wani dan Najeriya ya sata ta yanar gizo

Yadda Yariman Saudiyya ke son kawo sauyi a kasar

A shekarar 2017, lokacin da Yarima Muhammad ya fara aikinsa ne ya sanar da rage adadin takura da kakabawa mata takunkumi a kasar.

Wannan sanarwa ta jawo cece-kuce a idon duniya, musamman masu yiwa Saudiyya kallon kasar da ta zama cibiya ta yada addinin Islama.

Ko a masallatai, Yariman ya tabbatar da rage raka'o'in sallar Tarawiy a Ramadana tare da takaita saukin amsa-kuwwa a masallatai lokacin sallah.

An rage farashin lasasin kafa gidan fim a Saudiyya

A wani labarin, kun ji yadda kasar Saudiyya ta sakewa masu gidajen fim mara wajen samun lasisin kafa kallo a kasar.

Ragin kudin ya shafi kudin bude gidajen fim din da kuma gudanar da gidajen fim na din-din-din da kuma na wucin gadi.

A cewar jaridar Arab News, hukumar kula da fina-finai ta kasar ta sanar da cewa an rage kudin lasisin gidaje fim na dindindin a birane masu darajar A daga riyal 210,000 zuwa riyal 25,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel