Majalisa Ta Dauki Muhimmin Mataki Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro a Jihar Arewa

Majalisa Ta Dauki Muhimmin Mataki Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro a Jihar Arewa

  • Majalisar wakilai ta tashi tsaye domin maganace rikicin da ke aukuwa a jihar Plateau wanda ya halaka mutane masu yawa
  • Majalisar ta amince da kafa wani kwamiti wanda zai binciki musabbabin kai hare-haren na ta'addanci da ake yi a wasu ƙananan hukumomin jihar
  • Kafa kwamitin dai ya biyo bayan wani ƙuduri da wasu ƴan majalisa biyu na jihar ta Plateau suka gabatar a zauren majalisar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta amince da kafa wani kwamiti da zai binciki musabbabin hare-haren ta’addancin da aka kai a ƙananan hukumomin Mangu, Bokkos, Barkin Ladi da Riyom na jihar Plateau.

Amincewar ta biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa Ishaya David Lalu da ɗan majalisa Dalyop Fom Chollom suka gabatar a zauren majalisar a ranar Talata, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da babban dan kasuwa a jihar Arewa

Majalisa ta kafa kwamiti kan rikicin Plateau
Majalisar wakilai ta kafa kwamiti kan rikcin jihar Plateau Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Da suke gabatar da ƙudirin, ƴan majalisar sun ce an kai hari kan al’ummar ƙaramar hukumar Mangu a ranar 24 ga watan Janairu, 2024, inda aka kashe sama da mutane 50 yayin da wasu suka samu munanan raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ƙara da cewa:

"Sama da gidaje 1,000 da kadarori na biliyoyin nairori sun lalace gaba ɗaya inda mutane kusan 20,000 suka rasa matsugunansu inda suka koma sansanonin ƴan gudun hijira daban-daban a ciki da wajen yankin.
"Yawancin waɗanda suka samu raunuka daban-daban a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban na jihar.
"Hare-haren da ƴan ta’addan ke ci gaba da kaiwa a ƙaramar hukumar na buƙatar a gaggauta magance su."

Wane mataki majalisar ta ɗauka?

Majalisar ta buƙaci babban hafsan tsaron ƙasar da ya kafa rundunar haɗin gwiwa ta farar hula a jihar Plateau tare da umartar kwamitocin tsaro da bin doka da oda su tabbatar an yi hakan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

Ana sa ran za su riƙa ba majalisar rahoton mako-mako har sai an shawo kan matsalar rashin tsaron.

Jaridar Vanguard ta ce a zaman majalisar na ranar Talata, ta kuma buƙaci shugaban hukumar Kwastam ya bayyana a gabanta kan gaza bayyana bayanin shige da ficen kuɗin hukumar na shekara uku.

Ɗan Majalisa Ya Sharɓi Kuka Yayin Zaman Majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kakakin majalisar wakilai ya kece da kuka ana tsaka da zaman majalisa.

Akin Rotimi ya kece da kuka ne yayin da ake gabatar ƙudiri a gaban majalisar kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng