Matsalar Tsaro: Birnin Tarayya Abuja Na Fuskantar Babbar Barazana, Majalisar Dattawa Ta Magantu

Matsalar Tsaro: Birnin Tarayya Abuja Na Fuskantar Babbar Barazana, Majalisar Dattawa Ta Magantu

  • Majalisar dattawa ta bayyana cewa birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazanar rashin tsaro
  • Sanata Godswill Akpabio ya ce sun samu rahotannin yadda ƴan bindiga ke kwarara zuwa wasu yankunan FCT
  • Ya ce lamarin tsaro ya ƙara dagulewa a sassan ƙasar nan, inda ya bada misali da abin da ya auku a jihar Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya, ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, ta nuna matuƙar damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a kasar nan.

Majalisar ta ayyana cewa babban birnin tarayya Abuja wurin da kujerar mulkin ƙasar take na fuskantar barazana, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ɗauki muhimmin mataki da nufin gyara yadda ake zaɓe a Najeriya

Shugsban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Abuja: "Babban Birnin Tarayya Na Fuskantar Barazana Mai Muni" Majalisar Dattawa Hoto: Senator Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce mahara sun kutsa cikin Abuja, inda ya kafa hujja da hare-haren da aka kai a wurare kamar Kubwa, Bwari da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya yi wannan furucin ne gabanin majalisar ta ɗage zaman da ta shirya da hafsoshin tsaro saboda rashin halartar mai bada shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Rubadu da babban hafsan soji.

Majalisar ta fara ɗaukar matakai

A makon jiya ne majalisa ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro domin yi mata bayani kan matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya da kuma kokarin da suke na magance ta, in ji Channels tv.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane a sassan kasar nan, wanda ya hada da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Majalisar dattawa ta yi amai ta lashe, ta aike da saƙo ga NSA da wasu ministoci 3

Da yake jawabi gabanin dage taron, shugaban majalisar dattawan ya ce:

"Lamarin na kara cakuɗewa a Agatu, Taraba, Oyo, Mangu, Bokkos, Barkin Ladi. Mun kuma samu labarin kwararar ('yan bindiga) zuwa cikin babban birni (FCT) a wurare kamar Kubwa da Bwari.
"Mun samu rahoton suna da wurin da suke tattaruwa, sannan mun ji cewa hafsoshin tsaro da hukumomin tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu.
"To amma waɗannan rahotanni na kutsen ƴan ta'adda na ɗaga wa kowa hankali shiyasa muka yanke gayyato ku domin ku mana bayanin ƙoƙarin da kuke na magance matsalar "

Zanga-zanga ta kara ɓallewa a Neja

A wani rahoton kuma Kwana biyu bayan abinda ya auku a Minna, sabuwar zanga-zanga ta kuma ɓallewa a Suleja duk a jihar Neja.

Mata, maza da matasa sun toshe manyan tituna lamarin da ya jawo wa matafiya tsaiko na tsawon awanni yau Laraba

Asali: Legit.ng

Online view pixel