Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Zaben Gwamnan Jihar Delta

Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Zaben Gwamnan Jihar Delta

Kotun Koli ta yi zama na karshe kan karar da jam'iyyar APC da dan takararta, Ovie Omo-Agege, suka shigar kan Sheriff Omorevwori, gwamnan jihar Delta.

A karar da APC da dan takararta suka shigar, sun nemi kotu ta tsige gwamnan wanda ya yi takara karkashin jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar na watan Maris 2023.

A yau Juma'a, 19 ga watan Janairu, Kotun Koli ta yi watsi da wannan bukatar da tsohon mataimakin shugaba majalisar dattawan ya shigar gabanta, TVC News ta ruwaito.

A cewar kotun, jam'iyyar APC da Omo-Agege sun gaza kare tuhume-tuhumen da suke yi na cewar an tafka kura-kurai a zaben jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel