Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Ƴan Ta'adda, Sun Sheƙe Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Ƴan Ta'adda, Sun Sheƙe Masu Yawa

  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana gagarumar nasarar da dakarun sojoji suka samu cikin mako ɗaya
  • DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda 185 da cafke masu aikata laifuka mutim 212
  • Sojojin sun kuma ƙwato makamai da alburusai masu tarin yawa daga hannun ƴan miyagun ƴan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarar da dakarun sojojin ƙasar nan suka samu a cikin mako ɗaya.

DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kashe ƴan ta'adda 185, da cafke mutum 212 da ake zargi da aikata laifuka tare da kuɓutar da mutum 71 da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar nan, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kasurgumin shugaban ƴan bindiga a Arewa, sun ceto mutum 20 da aka sace

Sojoji sun sheke ƴan ta'adda
Dakarun sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 2 ga watan Fabrairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba ya ce mummunar ɗabi’ar garkuwa da mutane ta dusashe hasken nasarorin da sojoji ke samu wajen yaƙar ƴan ta’adda, masu tayar da ƙayar baya a fadin ƙasar nan, rahoton The Nation ya tabbatar.

Wacce irin nasara sojojin suka samu kan ƴan ta'adda?

Sai dai ya ce sojojin sun cafke mutum 44 da ake zargin ɓarayin mai ne tare da ƙwato lita 815,980 ta ɗanyen mai na sata, lita 163,675 na AGO da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, da kuma lita 1,750 na DPK da kuɗinsu ya kai N1,065,885,050.00.

Daraktan ya ce sojojin sun ƙwato makamai iri-iri har guda 224 da alburusai iri-iri guda 2,337.

Ya ce sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 113, bindigar G3 guda ɗaya, bindigar PKT guda ɗaya, bindigu na gida guda 44, bindigogin gida guda biyu, bindigar berretta ɗaya, bindigogi 25, da abubuwan fashewa guda bakwai.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gwamnan PDP ya sanya dokar hana fita, bayanai sun fito

Sauran sun haɗa da harsasai 1,382 masu kaurin 7.62mm, harsasan NATO guda 387 masu kaurin 7.62mm, harsasai 74 masu kaurin 9mm, harsasan K2 guda 23, harsasai guda 111, kwankwon gidan harsasai 5,410 masu kaurin 7.62mm, jigida guda biyu ɗauke da harsasai 60 masu kaurin 7.62mm, jigida guda 21, motoci biyu, wayoyi 47, kuɗi N2.3m da sauran abubuwa.

Sojoji Sun Halaka Shugaban Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe wani shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Sojojin sun kuma ceto wasu mutum 20 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel