Gwamnatin Plateau Ta Sanya Dokar Hana Fita Na Tsawon Awanni 24, Bayanai Sun Fito
- Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, gwamnan jihar Plateau ya sanya dokar hana fita a jihar na tsawon awanni 24
- An kafa dokar ce a karamar hukumar Mangu da ke fama da matsalar tsaro fiye da ko ina a fadin jihar baki daya
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan jihar, Gyang Bere ya fitar a yau Talata 23 ga watan Janairu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 a jihar.
Dokar za ta shafi karamar hukumar Mangu da ke jihar wacce ta ke fama da hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane.
Mene dalilin sanya dokar?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnan jihar, Gyang Bere ya fitar a yau Talata 23 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bere ya ce daukar matakin ya zama dole ganin yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a yankin, cewar Punch.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna ya nemi shawarwari daga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro kafin daukar matakin.
"Ya bayyana cewa iya mutane masu aiki na musamman kadai ne za su iya zirga-zirga a karamar hukumar har sai yadda hali ya yi.
"Ya bukaci 'yan jihar musamman mazauna karamar hukumar Mangu da su bi dokar tare da taimakawa jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya."
Gwamnan ya koka kan yadda wasu ke kokarin kawo cikas a zaman lafiya a jihar duk da kokarin da gwamnati ke yi, cewar Channels TV.
Martanin gwamnan jihar
Ya kara da cewa:
"Ya koka kan yadda wasu suka kirkiri rashin tsaro a jihar duk da kokarin gwamnatin jihar don ganin ta dakile ayyukan 'yan ta'adda.
"Ya tura sakon jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa inda ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya a jihar."
Gwamnan har ila yau, ya yi alkawarin sassauta dokar da zarar an samu zaman lafiya ya inganta a yankin, cewar Leadership.
'Yan Majalisu sun sha alwashin komawa kujerunsu
Kun ji cewa 'yan Majalisun jihar Plateau sun sha alwashin komawa kan kujerunsu saboda rashin adalci a hukunci kotu.
'Yan Majalisun 16 sun sha alwashin halartar zaman Majalisar a yau Talata 23 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng