Shugaba Tinubu Ya Nada Ali Nuhu Mukamin Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Nada Ali Nuhu Mukamin Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya

  • Ma'aikatar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira ta tarayya ta kara inganta tare da sabbin daraktoci guda 11
  • An nada wadannan sabbin daraktoci ne bisa ga umurnin Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da nadin nasu a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, kamar yadda Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin daraktoci 11 a ma'aikatar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira.

Wadannan daraktoci za su shugabanci hukumomi daban-daban a karkashin ma'aikatar, ciki harda majalisar kula da fasaha da al’adu ta kasa, hukumar tace fina-finai ta kasa, da kuma gidan tarihi na kasa.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunaye: Abba Yusuf, Caleb Mutfwang da gwamnoni 8 da Kotun Koli ta tabbatyar da nasarorinsu

Tinubu ya nada sabbin daraktoci
Tinubu Ya Nada Ali Nuhu, Obi Asika da Wasu 9 a Matsayin Daraktoci a Ma’aikatar Al’adu Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Su wanene sabbin daraktocin da aka nada?

Kamar yadda yake kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, daraktocin sun hada da:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

(1) Tola Akerele — Darakta Janar, Cibiyar al'adu ta kasa

(2) Dr Shaibu Husseini — Darakta Janar na Hukumar Tace Fina-Finai ta Kasa

(3) Mista Obi Asika - Darakta Janar na Majalisar al'adu ta kasa

(4) Aisha Adamu Augie — Darakta Janar na Cibiyar al’adun bakar fata da Afirka

(5) Ekpolador-Ebi Koinyan — Shugaban gidan ajiye kayan yaki na tarihi

(7) Chaliya Shagaya — Darakta Janar, makarantar kayan tarihi na kasa

(8) Hajiya Khaltume Bulama Gana — Babban daraktan gidan rawa ta kasa

10) Ali Nuhu — Shugaban Cibiyar fina-finai na Najeriya

(11) Ramatu Abonbo Mohammed - Darakta Janar, Hukumar kula da gidajen tarihi da abubuwan tarihi ta kasa

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da N-Power, Tinubu ya dauki matakin karshe kan shirin NSIPA, ya fadi dalili

Sanarwar ta bayyana cewa, shugaban kasar ya umurci wadanda aka nada da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da bin ka’idoji bisa kwarewa, kwazo da kishin kasa.

Manufar ita ce habbakawa da karfafa bangaren fikira.

Tinubu ya dakatar da shirin NSIPA

A gefe guda, mun ji a baya cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta kasa (NSIPA) ke gudanarwa, rahoton Leadership.

Daraktan labarai a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel