Gungun Matasa Sun Cinna Wa Gidan Yayar Mai Sarautar Gargajiya a Arewa Wuta, Ta Rasu da Jikarta
- Attah na Igala, Alaji Mathew Opaluwa ya kadu bayan wasu mutane sun cinna wa ‘yar uwarsa wuta a gidanta
- Aika-aikar matasan ya yi sanadin mutuwar dattijuwa mai shekaru 75 da kuma jikarta mai shekaru biyar
- Marigayiyar mai suna Meimunat Opaluwa ta rasa ranta ne da jikarta bayan sun cinna wa gidanta wuta a Okete-Ekwe a jihar Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi – Wasu matasa sun cinna wa gidan wata mata wuta inda suka yi ajalinta da jikarta mai shekaru biyar.
Marigayiyar mai suna Meimunat Opaluwa ta rasa ranta ne da jikarta bayan sun cinna wa gidanta wuta a Okete-Ekwe a jihar Kogi.
Wace ce marigayiyar kafin rasuwarta?
Meimunat ta kasance ‘yar uwa ga Mai Girma Attah na Igala, Alaji Mathew Opaluwa da ke jihar Kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu inda wadanda ake zargin suka watsa man fetur kafin cinna wutar a gidan.
Dalilin aika-aikar tasu ya yi sanadin mutuwar matar mai shekaru 75 da kuma jikarta mai suna Onechejo.
Daya daga cikin ‘ya’yan matar, Hajaratu Usman Sani wacce ke cikin dakin lokacin da abin ya faru ta na cikin mummunan hali.
Wata majiya ta tabbatar wa Daily Trust cewa wasu mutane ne suka zo da fetur a hannunsu lokacin matar ta na tare da jikarta a cikin dakin.
Mene martanin 'yan sanda a Kogi?
Wani daga cikin makusantan marigayiyar ya ce:
“Sun watsa fetur din a cikin dakin ta taga inda daga bisani suka cinna wuta da ya yi ajalin tsohuwar nan take.”
Marigayiyar a baya bayan nan aka bata sarautar gargajiya ta Iye Agwuma Attah ta Igala a shekarar 2023, cewar Daily Post.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Williams Aya ya ce har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba su samu bayani kan lamarin ba.
Boko Haram sun hallaka Fasto a Yobe
A wani labarin, Mayakan Boko Haram sun yi ajalin wani Fasto da wasu mutane biyu a wani hari da suka kai a yau Juma’a.
Marigayin mai suna Luka Levong ya gamu da tsautsayin ne bayan mayakan sun kai harin a garin Kwari da karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Asali: Legit.ng