Kirsimeti: Gwamnan Arewa Ya Ba da Hutun Kwanaki 7 a Jiharsa, Ya Tanadi Tulin Abinci Ga Al’umma

Kirsimeti: Gwamnan Arewa Ya Ba da Hutun Kwanaki 7 a Jiharsa, Ya Tanadi Tulin Abinci Ga Al’umma

  • Gwamna Umar Bago na jihar Niger ya ba da hutun kwanaki bakwai ga ma’aikatan jihar don su yi bukukuwan Kirsimeti
  • Bago ya bayyana haka ne yayin ganawa da mambobin Majalisar Zartarwar jihar a yau Laraba a birnin Minna da ke jihar
  • Ya ce ma’aikata za su yi hutu har na tsawon kwanaki bakwai wanda zai ba su damar yin bikin da kuma na sabuwar shekara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger – Gwamnatin jihar Niger ta ba da hutun kwanaki bakwai don bukuwan Kirsimeti da ake shirin yi a ranar Litinin 25 ga watan Disamba.

Gwamna Umar Bago na jihar shi ya bayyana haka yayin taron Majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a Minna, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC ya ba ma'aikata hutun kwanaki 14

Gwamnan APC zai gwangwaje ma'aikata yayin bikin Kirsimeti
Kirsimeti: Gwamna Bago ya ba da hutun kwanaki bakwai a jihar niger. Hoto: Umar M. Bago.
Asali: Facebook

Mene Bago ya ce kan bikin Kirsimeti?

Ya ce ma’aikata za su yi hutu har na tsawon kwanaki bakwai wanda zai ba su damar yin bikin da kuma na sabuwar shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya ce hutun zai fara ne daga ranar Juma’a 22 ga watan Disamba zuwa Litinin 1 ga watan Janairu, cewar Daily Post.

Gwamnan ya kuma ce za a ba da abinci ga makarraban gwamnati don raba wa marasa karfi a Unguwanninsu da kuma kananan hukumomi.

Mene Gwamna Otu ya yi jiharsa kan Kirsimeti?

Har ila yau, Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River ya bai wa ma’aikata hutun kwanaki 14 don bukukuwan Kirsimeti.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Emmanuel Ogbeche ya fitar a yau Laraba 20 ga watan Disamba.

Emmanuel ya ce hutun zai fara ne daga ranar Laraba 20 ga watan Disamba zuwa Talata 2 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

Sai dai ya bayyana cewa wannan bai shafi masu ayyuka na musamman ba da su ke aiki ba dare ba rana.

Gwamna Fubara ya bai wa ma’aikata kyauta

A wani labarin, Gwamna Sim Fubara a jihar Rivers ya amince da biyan naira dubu 100 kyauta ga ma’aikata a jihar.

Wannan kyautar na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti a kasar baki daya a ranar Litinin 25 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel