Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC Ya Ba Ma’aikata Hutun Kwanaki 14

Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC Ya Ba Ma’aikata Hutun Kwanaki 14

  • Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River ya amince da hutun kwanaki 14 ga dukkan ma'aikatan gwamnati a jihar wanda zai fara daga Laraba, 20 ga watan Disamba
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaran gwamnan, Emmanuel Ogbeche, ya gabatarwa manema labarai
  • Gwamnan ya bai wa ma'aikata wannan hutun ne domin su samu damar yin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara tare da iyalansu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Calabar, jihar Cross River - Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya amince da tsawaita hutun ma'aikatan gwamnati a jihar.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaransa, Emmanuel Ogbeche ya saki ya amince da Laraba, 20 ga watan Disamba zuwa Talata, 2 ga watan Janairun 2024, a matsayin hutu, illa ga wadanda ke ayyuka na musamman, AIT ta rahoto.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnati ta amince da kyauta mai gwabi ga ma'aikata domin Kirsimeti

Gwamnan Cross River ya ba ma'aikata hutun kwanaki 14
Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC Ya Ba Ma’aikata Hutun Kwanaki 14 Hoto: @officialspbo
Asali: Twitter

Cross River: Otu ya ba da hutun kwanaki 14 don bikin Kirsimeti

Gwamnan ya bukaci ma'aikatan gwamnati da su yi amfani da damar wajen kula da iyalinsu, yayin da ya kuma bukace su da su shiga bikin karshen shekara da ake yi na Calabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada jajircewar gwamnatinsa wajen samar da yanayi mai kyau ga dukkan al'umma da mazauna jihar yayin da yake taya su murnar bikin Kirsimeti da sabuwar shekara mai inganci, rahoton The Cable.

Tinubu ya yiwa yan Najeriya tagomashi

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabtare farashin ababen hawa da kaso 50% a tafiye-tafiyen jiha zuwa jiha a fadin Najeriya.

Haka zalika, shugaban kasar ya ba da umurnin cire kudin hawan jirgin kasa, wanda ke nufin matafiya za su hau jirgin kasa kyauta.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya gana da Tinubu da shugaban alkalai kan hukuncin Kotun Koli? gaskiya ta bayyana

Tinubu ya dauki wannan matakin ne don saukaka wa 'yan Najeriya a yayin da su ke shirye-shiryen bikin kirsimeti da sabuwar shekara.

Gwamnan Ribas ya gwangwaje ma'aikata

A gefe gudu, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ya amince da Naira 100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga ma’aikatan jihar.

Warisenibo Joe Johnson, kwamishinan yada labarai da sadarwa, ya ba da wannan bayanin kwanaki shida kafin zuwan Kirsimeti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel