Mahalarta Biki Sun Cika da Murna Yayin da Aka Raba Masu Kyautar Biredi, Bidiyon Ya Yadu

Mahalarta Biki Sun Cika da Murna Yayin da Aka Raba Masu Kyautar Biredi, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yada wani bidiyo da ke nuna cewa iyalinta sun dauki gudunmawar biredi zuwa wani biki sannan suka rabawa jama'a
  • Matashiyar, Ogtomisin, ta ce iyalinta sun rabawa mutane biredin a matsayin kyauta a wajen bikin
  • An gano mahalarta bikin rike da biredi da yawansu ya kai biyar dauke da murmushi a fuskokinsu, wanda ke nuna sun yi farin ciki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jama'a sun cika da farin ciki a wajen wani biki lokacin da wasu iyali suka raba biredi a matsayin kyauta a wajen taron.

An yi wa ledan biredin tambari na musamman wanda zai yi daidai da bikin dauke da taken 'Divine Agege Bread' rubuce a jiki.

Kara karanta wannan

"Ku daina auren talakawan mata da ba za su iya ba ku kudi ba": Daddy Freeze ya shawarci maza

An yi rabon biredi a wajen biki
Mahalarta Biki Sun Cika da Murna Yayin da Aka Raba Masu Kyautar Biredi, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@ogtomisin.
Asali: TikTok

Mahalarta bikin sun cika da farin ciki ganin cewa za su je gida da sinkin biredi yayin da suka baje kolinsu bayan sun samu rabonsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mutanen sun karbi sama da guda daya, wanda ke nuna cewa hakan ya samu karbuwa sosai.

Da take yada bidiyon, Ogtomisin, ta ce iyalinta ne suka shirya biredin sannan suka raba shi a matsayin gudunmawa a wajen bikin.

Ta yi wa bidiyon take da:

"Divine Agege bread ya sake bayyana. Bugun bikin aure."

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da aka raba biredi a wajen biki

@mursee ta ce:

"3 ba za su baci ba kafin ya gama da 2?"

@notmaz ta ce:

"Shin wannan na cikin sadakin ne?"

@sisibiko ta ce:

"Biredin Agege yana da karfi."

@BigDebo ta yi martani:

"Tafiya da guda 5 rashin hankali ne."

Kara karanta wannan

"Sun yi zaton damfara nake yi": Mai aiki a gidan mai ta dau wanka ta bayan aiki, bidiyon ya yadu

@BarbTemz ta ce:

"Ina son zuwa bikin Najeriya. Kyaututtukan da ake rabawa wajen bikin babu irinsu."

@Remi ta ce:

"Don Allah miko daya. Zan yi amfani da shi wajen cin biredi."

Budurwa ta rabu da saurayi saboda biredi

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa wata budurwa ƴar Najeriya mai amfani da sunan @kaaego a kan manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter) ta faɗi dalilin da ya sa ta daina kula wani da ya nuna yana sonta.

A cewarta, dole ce ta sanya cikin gaggawa ta yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninta da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel