Yunwa Babu Dadi: Bidiyon Matasa Suna Murna Bayan Mai Shago Yayi Sadakar Biredi

Yunwa Babu Dadi: Bidiyon Matasa Suna Murna Bayan Mai Shago Yayi Sadakar Biredi

  • Wani mai tireda 'dan Najeriya yayi rabon dukkan biredin dake shagonsa ga kwastomominsa inda yace kada su biya shi ko sisi
  • 'Dan kasuwan daga baya ya bayyana cewa wani ne dake kallonsa daga TikTok a kai tsaye ya biya dukkan kudin kuma yace ya raba kyauta
  • Kwastomominsa sun matukar shan mamaki yayin da suka samu kyautar ba-zatan inda suka dinga kiran 'yan uwansu da su zo su karba garabasar

Wani matashi 'dan Najeriya ma'abocin amfani da TikTok ya yi bidiyon kai tsaye inda ya bayyana lokacin da yake raba biredi kyauta ga kwastomominsa daga shagonsa.

'Dan kasuwar yace yana wannan bidiyon na kai tsaye lokacin da wani mutum yace ya siya dukkan biredin shagonsa kuma yace ya rabawa jama'a ba tare da ya karba ko sisinsu ba.

Bread
Yunwa Babu Dadi: Bidiyon Matasa Suna Murna Bayan Mai Shago Yayi Sadakar Biredi. Hoto daga TikTok/@d_editor02
Asali: UGC

Kyautar Biredi

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

A yayin karbar sunkin biredin da ya ba kwastomomin, sun dinga kiran wasu jama'a da su garzayo shagon don samun rabonsu. Wasu jama'a kuwa sun sha mamaki ta yadda suka saki baki suka kasa karbar biredin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran kuwa da suka karba kyautarsu din sun kira abokanansu da su garzayo su karba nasu. Ya bayyana cewa tsofafin da yake bi bashi ne kadai suka ki zuwa karba.

Kalla bidiyon:

Jama'a sun yi martani

Tuni 'yan Najeriya suka garzaya tare da fara yin martani kan wannan lamarin. Ga wasu daga cikin tsokacin da Legit.ng ta tattaro:

Eric Okafor yace:

"Wannan ne abinda ban san cewa ya dace in gan shi ya ba."

D_parasite yace:

"Wannan babu shakka zai sa ka samu karin kwastomomi. Abu yayi kyau."

Ibidabo Jonah yace:

Kara karanta wannan

Yancin Kai: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Shirya Taron Addu'o'i Na Don Najeriya, Ya Mika Sako Ga Yan Siyasa

"Allah ya albarkaci wanda ya dauka nauyi."

Louis Hizik yace:

"Ina matukar kaunar gayen nan."

Kishiya Da Dangin Miji Ne Suka Saka Ni Gaba Da Gori, Matar Da Ta Sace Jinjiri Daga Asibiti

A wani labari na daban, jami’an tsaron farin kaya sun dam ke wata mata kan zarginta da sace jaririn kwana takwas mai suna Ibrahim Mohammed daga asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

Yaron da aka samo daga wacce ake zargin an mika shi ga iyalansa a ranar Talata, jaridar Punch ta rahoto.

Wacce ake zargin ta yi basaja a matsayin ma’aikaciyar jinya sannan ta aikata laifin. Kamar yadda majiyar tace, wacce ake zargin ta sace jinjirin ne saboda yadda kishiyarta da dangin mijinta ke mata gori saboda rashin haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel