Ayiriri: Jaruma Rashida Mai Sa'a Za Ta Shiga Daga Ciki a Ranar Asabar Mai Zuwa

Ayiriri: Jaruma Rashida Mai Sa'a Za Ta Shiga Daga Ciki a Ranar Asabar Mai Zuwa

  • Labari da ke zuwa daga masana'antar Kannywood shi ne batun amarcewar da jaruma Rashida Mai Sa'a za ta yi a ranar Asabar mai zuwa
  • Za a kulla aure tsakanin ashida Adamu da angonta Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan matasan Gwoza
  • Za a daura auren jarumar a unguwar Malam Bello da ke Daurawa, Maiduguri Road, a jihar Kano

Labari mai dadi daga masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood shine batun auren fitacciyar jaruma Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida Mai Sa'a.

Rashida mai sa'a za ta yi aure
Ayiriri: Jaruma Rashida Mai Sa'a Za Ta Shiga Daga Ciki a Ranar Asabar Mai Zuwa Hoto: Kannywood
Asali: Facebook

Za a daura auren Rashida da angonta mai suna Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan matasan Gwoza a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda dandalin Kannywood ya wallafa a Facebook, za a daura auren jarumar ne a unguwar Malam Bello da ke Daurawa, Maiduguri Road, a jihar Kano

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya bayyana mafita 1 tak ga matsalolin Najeriya

Jama'a sun yi martani kan batun auren jaruma Rashida

Sadi Muhammad ya yi martani:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kuna auren masu kudi ko sai kunja abin da kukaja sai kusa su sakeku Dan gutsun ubanku ko wani sain har kuna cewa kundaina aure amma idan anga mai kudi sai ayi saboda kudinsa."

Aisha Usman Jos ta yi martani:

"Allah ya sanya alheri."

Murjanatu Shu'aibu ta ce:

"Lakaci mudu ne, Ma hakurci ma wada ci, Fatan alheri."

Fateemah Adam ta ce:

"Masha Allah, dama komai lkc ne."

Suraja Abban Sauban Grm ya ce:

"Fatan Al Khairy Baki Dayah"

Asiah Elsurajh ta yi martani:

"Allah yasanya Alkairi yazaunar dasu lpia."

Fatima Aminu Ahmad ta ce:

"Mashaa Allah. Allah ya sanya alkhairi ya sa a zauna lfy."

Nana Isah ta ce:

"Anna ba shekarar bara ko shekarar nan naji tayi aure ba."

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Mohammed Hafsat ta ce:

"Masha Allah na tayaki murna Allah ya Sanya Alkhairi."

Safiyya Muhammad ta ce:

"Mashaa Allah, Allah yasanya alkhairi yasa ayi a sa'a."

An yi shagalin biki da hoton ango

A wani labarin, mun ji cewa masu amfani da soshiyal midiya sun girgiza da wani sabon salon biki da aka yi.

An sha shagalin bikin wata amarya da hoton angonta da baya gari. Don nuna biyayya gare shi tamkar yana nan, amaryar ta durkusa a gaban hoton angon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel