“Sun Yi Zaton Damfara Nake Yi”: Mai Aiki a Gidan Mai Ta Dau Wanka Bayan Aiki, Bidiyon Ya Yadu

“Sun Yi Zaton Damfara Nake Yi”: Mai Aiki a Gidan Mai Ta Dau Wanka Bayan Aiki, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata mai aiki a gidan mai ta baje kolin kyawunta a wani bidiyon TikTok da ya yadu
  • An gano matashiyar a gidan mai inda take zubawa wani kwastama mai a galan, sannan yan sakanni bayan nan, ta sauya ta koma kasaitacciyar budurwa
  • Mai aiki a gidan man ta ce wasu suna yi mata kallon yar damfara saboda yadda take sheki da walwali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wata matashiyar budurwa wacce mutane ke yi mata mummunar fassara. Ta ce wasu suna yi mata kallon yar damfara saboda yanayin shigarta.

A cikin bidiyon, matashiyar ta fito fili ta bayyana cewa aikin siyar da mai take yi a gidan man.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Budurwa na siyar da mai
“Sun Yi Zaton Damfara Nake Yi”: Mai Aiki a Gidan Mai Ta Dau Wanka Bayan Aiki, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@thacute_sommie.
Asali: TikTok

An gano matashiyar, @thacute_sommie, tana kula da kwastamomi da suka zo siyan mai a gidan man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani wurin kuma, an nuno lokacin da ta kammala aiki sannan ta sauya zuwa wata kasaitacciyar budurwa.

Sommie ta shiga wani yayi da ake yi a TikTok inda mutane ke nuna kansu a wajen aiki da kuma yadda suke bayan aiki.

Duk da yanayin shigarta mai daukar ido, Sommie ta yi ikirarin cewa tsawon watanni hudu kenan bata samu albashi ba.

Kalli bdiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Amaka ta ce:

"Baya ga haka, ka ga masu aikin zuba mai, mutanen nan na da kudi. Idan ka sani ka sani."

@Abike ta yi martani:

"Ka ga masu zuba mai da masu karban kudi a gidan caca, mutanen nan na da kudi."

Kara karanta wannan

"Tsohuwar dalibata yanzu amaryar mijina": Matar aure ta magantu yayin da mijinta ya kara aure

@Oladimeji Nofisat ta ce:

"Ni mai aikin zuba mai ce na san yadda abun yake."

@user54847353741 ya ce:

"Mai siyar da mai da rana sannan.... da daddare Allah ya albarkaci nemanki yar'uwata."

Budurwa ta mika kokon barar soyayyarta

A wani labari na daban, mun ji cewa hadimin shahararren mawakin Najeriya Davido, Isreal Afaere wanda aka fi sani da Isreal DMW, ya hau kanen labarai saboda mutuwar aurensa.

Wata matashiyar budurwa, Ella Ada, ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin fallasa sirrin zuciyarta na irin son da take yi wa Isreal yayin da ta roke shi da ya taimaka ya aureta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel