“Wannan Aure Akwai Matsala”: Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

“Wannan Aure Akwai Matsala”: Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon da ke nuna wani al'amari mai rikitarwa da ya afku a wajen wani shagalin biki
  • An gano ango da amarya suna kiciniyar fita ta kofa a lokaci guda kuma kowannensu ya ki bari dayansu ya fara wucewa
  • Yayin da mutane da dama suka caccaki angon a kan kin nuna dattako, wasu sun nuna damuwarsu a kan amaryar

Wani bidiyon amarya da ango suna kiciniyar fita daga kofa a lokaci guda ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Shafin @axmedzaki440 ne ya wallafa bidiyon mai rikitarwa a dandalin TikTok kuma ya samu kimanin mutum miliyan 14.5 da suka kalla a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Ango da amarya na fada a ranar aure
“Wannan Aure Akwai Matsala”: Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa Hoto: @axmedzaki440
Asali: TikTok

A bidiyon, angon ki ja baya domin amaryarsa ta wuce yayin da suke fafutukar fita daga wani dan karamin kofar kwano a tare.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Ajiye Girman Kai, Ya Roki Budurwarsa Ta Hanyar Birgima a Kasa, Bidiyon Ya Bazu

Ana haka, angon ya murkushe amaryar don riga ta fita daga kofar. Sannan ya yi mata wani irin kallo na za ki yi bayani tare da yi mata magana cikin wani irin siga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun caccaki angon kan kin barin amaryar tasa ta fara fita.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun caccakin angon

Little_Maame:

"Ban ga kowa yana cewa Allah ya yi masa irin tasu ba."

Maryannqueenofficial ta ce:

"Shiyasa bana gaggawan aure.....Ina bukatar kasancewa cikin farin ciki ba wai na sanya al'umma farin ciki da sunan aure ba."

user9613995500663 ya ce:

"Me yasa bai bari ta fara fita ba? Dukkansu suna fafutukar fara fita waje."

DJ Fago ya ce:

"Gayen na cikin firgici sannan yana tambayarta me yasa take tsoro."

Rahel ta ce:

"Idan bai mutunta ta daga farko ba me zai faru kenan? ki gudu yar'uwa."

Kara karanta wannan

“Na Zata Farfadiya Ce Da Shi”: Bidiyon Matashi Yana Gulma a Gidan Kitso Ya Girgiza Mata

Lushell Hamilton265 ta ce:

"Me yasa ba zai nuna dattako sannan ya bari amaryar ta fara fita ba."

Tracy Tasha Bree:

"Wannan auren ya riga ya samu matsala. Ba zai iya bari ta fara fita ba har a ranar auren."

“Ana dole?” Wani mutum ya kwanta a kasa don rokon budurwarsa, ya kama kafarta

A wani labarin, a wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, an sha yar dirama yayin da aka gano wani mutum yana jan kansa a kasa yayin da yake rokon wata budurwa wacce ga dukkan alamu sahibarsa ce don kada a rabu da shi.

Bidiyon ya nuno wani mutum kwance a kasa, hawaye na ta kwaranya daga idanunsa yayin da ya rike kafar budurwar tasa, don baya so ta kufce masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel