Abubakar-Surajo Imam: Rundunar Sojin Najeriya Ta Samu Farfesa Na Farko, Bayanai Sun Fito

Abubakar-Surajo Imam: Rundunar Sojin Najeriya Ta Samu Farfesa Na Farko, Bayanai Sun Fito

  • An kafa tarihi a kwalejin horas da sojoji ta Najeriya inda aka samu mutum na farko da ya kai matsayin Farfesa
  • Laftanal-Kanal Abubakar-Surajo Imam ya zama Farfesa a fannin 'Mechatronics Engineering' na kwalejin
  • Haifaffen jihar Katsina, Imam ya shafe shekaru yana koyarwa a kwalejin inda ya bayar da gudunmawa mai tarin yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya, NDA, da ke Kaduna ta sanar da ƙarin girma ga Laftanal-Kanal Abubakar-Surajo Imam zuwa matsayin Farfesa a fannin 'Mechatronics Engineering'.

Mista Imam shi ne Farfesa na farko daga cikin ma'aikatan da ke aiki yanzu a tarihin rundunar sojojin Najeriya, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun kai samame maɓoyar 'yan bindiga akalla 5 a Arewa, sun samu gagarumar nasara

Imam ya zama Farfesa a Rundunar Sojin Najeriya
Imam Abubakar-Surajo ya zama Farfesa na farko a Rundunar Sojin Najeriya Hoto: Naufal Ahmed
Asali: Facebook

Magatakardan kwalejin, Birgediya-Janar AM Tukur ya sanar da ƙarin girman a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba a Kaduna, rahoton PM News ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an amince da ƙarin girman ne yayin taron majalisar zartaswar kwalejin NDA a watan Satumba, kuma ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Oktoban 2022.

Magatakardar ya ce matakin majalisar ya nuna ƙwarin gwiwa da amincewa da gudunmawar da Malam Imam ya bayar ga sashen 'Mechatronics Engineering' na kwalejin.

Ya ce sabon Farfesan ya samar da ayyuka na kwarai tare da tabbatar da ƙwazon da ake sa rai a fagen nasa.

"Wannan ƙarin girman ba wai kawai ya karrama Farfesa Imam ba ne, amma ya nuna jajircewar NDA wajen yarda da yin sakayya kan gudunmawar da aka bayar ta fannin ilmi a cikinta." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Wane Farfesa Abubakar-Surajo Imam

Malam Imam wanda ya fito daga Kankia a Jihar Katsina, ya yi digiri na farko a fannin 'Mechanical Engineering' a jami’ar Bayero da ke Kano.

Ya kuma yi Digiri na biyu a fannin Mechatronics daga jami’ar Newcastle da ke UK, sannan ya yi digiri na uku a fannin Mechatronics da Robotics daga Jami'ar ta Newcastle.

A halin yanzu ya na riƙe da matsayin shugaban, sashen 'Mechatronics Engineering' da daraktan cibiyar 'Centre for Innovation and Innovation' a kwalejin NDA.

Mai Tuka Baro Ya Zama Farfesa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani malamin jami'ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ya bayyana yadda ya fara da tuƙin baro da gyaran takalmi har zuwa matsayin Farfesa.

Nicholas Asogwa, wanda ke karantarwa a bangaren Falsafa, ya ba da labarin rayuwarsa a cikin wata takarda mai taken "Gwagwarmayata zuwa matakin farfesa" wanda ya karanto a wajen wani taro da aka yi don karrama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel