Jam'iyyar PDP Ta Rasa Ɗan Majalisa Ɗaya Tilo da Take da Shi a Jihar Arewa, Ya Koma APC

Jam'iyyar PDP Ta Rasa Ɗan Majalisa Ɗaya Tilo da Take da Shi a Jihar Arewa, Ya Koma APC

  • Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan majalisa ɗaya tilo da take da shi a majalisar dokokin jihar Yobe ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba
  • Lawan Majakura, matashin da ya lallasa tsohon kakakin majalisar a PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Ya bayyana cewa ya yanke ɗaukar wannan matakin ne bayan nazari kan irin ayyukan da Gwamna Buni yake zuba wa a mazaɓarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Ɗan majalisa ɗaya tilo da jam’iyyar PDP ke da shi a majalisar dokokin jihar Yobe, Honorabul Musa Lawan Majakura, ya sauya sheƙa zuwa APC.

Hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rawaito cewa Majakura, wanda ke wakiltar mazabar Nguru ta 2 a majalisar, ya koma jam’iyyar APC ne ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta tabbatar da sabon muhimmin naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi

Dan majalisar PDP ɗaya tilo a jihar Yobe ya koma APC.
Dan Majalisar PDP Guds Daya Tilo Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Hoto: Hassan Peppe Yobe State
Asali: Facebook

Da yake karbar dan majalisar a Damaturu, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana Majakura a matsayin matashi kuma hazikin dan siyasa mai dimbin basira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro Gwamna Buni na cewa:

“Siyasa ita ce hidima ga al'umma, na gamsu da jajircewar ka na yi wa jama'ar mazabarka hidima yadda ya kamata. Na kuma gamsu da irin halayen mutanen da suka rakoka zuwa wannan taron."
"Wannan ya nuna a fili cewa ka samu karbuwa hannu bibbiyu a wurin waɗan nan mutanen kirki."

Ko meyasa ɗan majalisar ya zaɓi komawa APC?

Tun da farko, Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa APC ne saboda gwamnatin Mala Buni na yi wa al’ummar mazabarsa ayyuka masu ɗumbin yawa.

Ya ce gine-ginen tituna, gidaje, wuraren kiwon lafiya da sauran ayyuka ya kawo sauyi ga al’umma da dama a mazabarsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

A rahoton jaridar Vanguard, ɗan majalisar ya ce:

“Ina son na taho mu hada kai kuma na baka goyon baya ɗari bisa ɗari wajen yi wa mazaba ta hidima domin inganta rayuwar al’ummata."

Kakakin majalisa ya yaba wa Majakura

A nasa jawabin, shugaban majalisar dokokin jihar Yobe, Chiroma Mashio, ya bayyana dan majalisar a matsayin babban mai kare muradun al’ummarsa.

"Sauya sheƙar da ya yi zuwa APC na da matuƙar amfani ga jam'iyyar da kuma Gwamnatin jihar Yobe," in ji shi.

Idan baku manta ba, Majakura, malamin makaranta mai shekaru 33, ya doke tsohon kakakin majalisar, Ahmed Mirwa, a zaben da aka yi ranar 18 ga Maris, 2023, inda ya zama sabon wakilin mazabar.

NNPP ta musannta yunkurin maja da wasu jam'iyyu

A wani rahoton kuma Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta nesanta kanta da kowace irin tattaunawar haɗa maja da wasu jam'iyyun siyasa.

Sakataren watsa labaran NNPP na ƙasa, Alhaji AbdulRazaq AbdulSalam, ya ce matakin da BoT ta ɗauka kan Kwankwaso na nan daram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel