Baiwa daga Allah: Bahaushen Kano ya kafa tarihi, ya zama makaho na farko da ya zama farfesa a Najeriya

Baiwa daga Allah: Bahaushen Kano ya kafa tarihi, ya zama makaho na farko da ya zama farfesa a Najeriya

Legit.ng ta ci karo da wani rahoto da ya ja hankalin jama'a a kan wani mutum dan asalin jihar Kano da ya kafa tarihi a bangaren harkar ilimi a Najeriya.

Mutumin mai suna Farfesa Jibrin Isah Diso, wanda aka haifa da larurar rashin gani (makanta), ya kai kololuwar ilimi a karatun Boko, wato ya samu lambar girma ta 'Farfesa' a tsangayar ilimi ta jami'ar Bayero da ke Kano.

Farfesa Diso, Bahaushen jihar Kano, ya zama makaho na farko da ya taba kai wa wannan matsayi a tarihin Najeriya.

Baiwa daga Allah: Bahaushen Kano ya kafa tarihi, ya zama makaho na farko da ya zama farfesa a Najeriya
Farfesa Jibrin Isa Diso
Asali: Facebook

Duk da kasancewarsa makaho, Farfesa Diso ya wallafa takardun bincike da kuma bayar da gudunmawa a bangarensa har guda 12.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel